Ƙungiyar da take ƙarfafawa mata gwuiwa domin ganin sun dogara da kansu ta “Mata Network’ za ta gudanar da taron ta da ta saba yi duk shekara a ranar bakwai ga watan Disamba a Kano.
Taron wanda ake haɗa shi domin ƙarfafawa mata gwuiwa ta hanyar ilimintarwa da koya musu dabaru haɗi da ƙulla hulɗar kasuwanci, zai kasance na shida kenan tun bayan kafa ƙungiyar, kuma za a yi shi ne a ɗakin taro na Meena event center da ke jihar Kano.
- Jawabin Shugaba Xi A Taron G20: Ya Kamata A Bar Adalci Ya Wanzu A Doron Kasa
- ‘Yansanda Sun Cafke Wadanda Suka Kulle Matashi A Kejin Kare
A jawabinta, Yasmin Obadaki, wadda ɗaya ce daga cikin waɗanda suka assasa wannan ƙungiya ta ce taron na bana zai banbanta da na shekarun baya domin an gayyato kwararrun da za su yi jawabai daban-daban a kan kasuwanci da yadda za a bunƙasa kasuwanci da tallata shi da kula da lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa.
Har ila yau, a cewar Yasmin, za a bayar da shawarwari a kan faɗaɗa kasuwanci, zamantakewar aure da sauran shawarwarin da mata suke buƙata a wannan lokaci domin ci gaban rayuwarsu.
Sannan za a horar da mata a kan yadda za su fara kasuwanci da abin da za su buƙata ta hanyar masanan da aka gayyato a sassa daban-daban na kasar nan.