An karasa sauran wasannin cikin rukuni ranar Talata a fafatawar neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a buga a 2025 a kasar Morocco, inda kawo yanzu an samu 24 da suka samu gurbin shiga babbar gasar ta Afirka.
Ranar Litinin aka samu karin tawagogin da suka samu damar shiga gasar da za a yi a badi, daga ciki har da Sudan da Benin, sannan kuma a makon jiya ne Nijeriya da Tunisia da Afirka ta Kudu da Uganda da Ekuatorial Guinea da kuma Gabon, suka samu gurbin shiga gasar ta AFCON.
- Hukumar FIFA Ta Dage Gasar Cin Kofin Afirka AFCON Zuwa Shekarar 2026
- AFCON 2023: Abubuwan Da Suka Faru Ga Super Eagles
Sauran da za su buga karawar ta Morocco har da Zambia da Mali da Zimbabwe da kuma Comoros sai mai masaukin baki, Morocco ta samu tikitin.
shiga gasar kai tsaye tare da Senegal da Algeria, wadanda suka taka rawar gani a rukuninsu.
Haka kuma Masar da Cote d’Iboire mai rike da kofin sun nuna da gaske suke a karawar da za a yi a badi, bayan kwazon da suka nuna a neman
shiga gasar wadda za a fara a cikin watan Dismbar shekara ta 2025.
Wasu kasashen da suka samu gurbi a wannan lokacin, wadanda ba su shiga gasar a baya ba, sun hada da DR Congo da Angola da Ekuatorial Guinea,
ya yin da Uganda da Gabon za su koma buga gasar da kwarin gwiwa sosai.
Afirka ta Kudu, wadda ta taka rawar gani a gasar kofin Afirka da aka yi a Ibory Coast, ita ma za ta kara a wasannin babbar gasar ta Afirka ta badi bayan ta taka rawar gani sosai a gasar cin kofin da ta gabata a kasar Ibory Coast.
Kasashe 21 da suka samu gurbin shiga gasar Afcon 2025:
Morocco mai masaukin baki Burkina Faso, Cameroon, Algeria, DR Congo, Senegal, Egypt, Angola, Ekuatorial Guinea, Cote d’Iboire, Uganda, South Africa, Gabon, Tunisia, Nigeria, Zambia, Mali Zimbabwe. Comoros, Sudan, Benin, Tanzania, Botswana, Mozambikue