Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli na G20 karo 19 a birnin Rio de Janeiro dake kasar Brazil, inda ya gabatar da ra’ayoyin Sin da shirin Sin kan yadda za a sa kaimi ga samun ci gaban duniya da kuma kyautata tsarin sarrafa harkokin duniya baki daya, wadanda kasa da kasa suka yaba musu sosai.
Farfesan tattalin arziki na kwalejin kimiyya da fasaha da jigila kaya cikin jiragen ruwa na Arab na kasar Masar Karim Ahmed Hamouda ya bayyana cewa, kasar Sin ta kasance misali na kawar da yunwa da talauci a duniya. Kasar Sin ta riga ta cimma burin fitar da matalauta miliyan 800 daga kangin talauci, da inganta rayuwar jama’ar kasar, kana kasar Sin ta bi manufar bude kofa ga kasashen waje, da more fasahohinta tare da kasashe masu tasowa, don yin kokarin taimakawa sauran kasashe wajen kawar da talauci, lamarin da ya samu nasarori da dama.
A gun taron kolin G20 na wannan karo, shugaba Xi Jinping ya gabatar da taswirar samun ci gaba ga kungiyar G20, shugaban cibiyar nazarin dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka na wannan zamani ta jami’ar Abuja ta kasar Najeriya, Sheriff Ghali Ibrahim ya bayyana cewa, bisa tsarin kungiyar G20, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugabannin sauran kasashe masu tasowa sun gabatar da ra’ayoyinsu game da bukatun kasashe masu tasowa na duniya, don sa kaimi ga bunkasa da kyautata tsarin kungiyar G20, wannan ce makomar bunkasuwar duniya. (Zainab Zhang)