Yayin taron manema labarai na yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce tun bayan ziyarar da Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan, sama da kasashe 160 sun bayyana goyon bayansu ga Sin tare da yin tir da ziyarar.
A cewarta, ziyartar Taiwan, tsokana ce da rashin sanin ya kamata, tana mai cewa, dukkan kasashen sun ce suna martaba manufar Sin daya tak a duniya, kuma suna goyon bayan Sin din wajen kare ‘yanci da iyakokinta. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)