Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta bankado tare da lalata wurin da ake samarwa da sarrafa muyagan kwayar a jihohin Legas da Anambra.
Hukumar ta ce kwayoyin suna da matukar illa tare da gusar da hanakalin masu ta’ammuli da ita da ake kira Mkpuru Mmiri, wadannan kamfanoni manya guda biyu da suke samarwa tare da rarraba wannan muyagan kwaya har da fita da su kasashen ketare.
- Sama Da Kasashe 160 Sun Bayyana Goyon Bayansu Ga Sin Tare Da Tsayawa A Bangaren Gaskiya Da Adalci
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Aike Da Sammaci Ga Wasu Jakadun Kasashen Turai Da Kungiyar EU Don Nuna Rashin Jin Dadinta
Shugaban hukumar NDLEA, Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa mai murabus ne ya bayyana haka a lokacin da yake tattauanawa da manema labarai game da ci gaban da aka samu a ranar Talata da ta gabata.
A cewarsa, sakamakon yaduwar wannan muyagan kwayar a yankin kudu maso gabashin Nijeriya ne a watanni uku na farkon shekarar 2021, ta yadda matasa da dama a yankin suka shiga ta’ammuli da wannan muyagan kwaya, sai hukumar ta shiga farautar wuraren da ake sarrafata su tare da bincike na musamman har aka bankado wurin da ake samarwa da kama masu safararta.
Marwa ya ce sun dauki kamar watanni bakwai suna farautar masu hannu a cikin lamarin, inda a yanzu suka yi nasarar cafke manyan masu ta’ammuli da ita su hudu; “a yanzu akwai masu safarar muyagan kwayoyi biyu da suka hada da su. Wannan babu tantama duk wanda suke gudanar da harkokin kasuwancinta za su rasa damar da suke da ita na zuba jarinsu a cikin haramtaccen kasuwanci.”
A cewarsa, “Ina mai farin cikin sanar da al’umma a yau cewa bayan watanni da suka yi suna gudanar da binciken sirri, mun sami nasarar kama masu aikata laifin muyagan kwayoyi a ranar Asabar da ta gabata, a lokacin da jami’an hukumar suka yi nasarar kai samame da tarwatsa inda ake samar da muyagan kwaya ta Mkpuru Mmiri da ake kira ‘Meth Laboratories.’
“Na farko yana rukunin gidajen bictoria Garden City (bGC) da ke Lekki cikin Jihar Legas, wanda fitatccen dillalin muyagun kwayoyin nan mai suna Chris Emeka Nzewi ya mallaka, sai kuma na biyun da ke garin Nise a karamar hukumar Awka ta Kudu a Jihar Anambra mallakar Paul Ozoemenam.
Tuni dai aka kama wadannan mutane guda biyu da suka mallaki wurin samar da wadannan miyagun kwayoyi tare da Sunday Ukah daga Aba Jihar Abiya wanda yake da dakin shan mugunguna da yake samar masu da kwayoyi.
“dakin sarrafa muyagun kwayoyi da ke Legas an tsara shi a cikin bangaren da yara suke zama da ake kira (Boys’ kuarter) a bayan gida mai dakuna hudu.
Daga nan ne muka samu jimillar sinadarai masu nauyin kilogram 258.74 da ake amfani da su wajen samar da kwayoyi masu gusar da hankulin masu amfani da su. An sami cikakkun kayayyakin aikin da ake amfani da su a dakunan da sundukin iskar gas da kuma sauran abubuwan amfani na yau da kullum da suke taimakawa wajen ayyukan samarwa”
Ya ce yana gabatar wa da al’umma wannan bayanai ne domin a wayar da kan mutane game da rushe wadannan daukan da jami’an hukumar suka yi a karshen mako.
Ya kuma kara da cewa, “Wanda ya mallaki dakin sarrafa miyagun kwayoyi na Jihar Legas yana samar da muyagan kwayoyi da suke kawar da hankulan al’umma a gidansa da yake zaune da iyalansa. Bai yi la’akari da irin cutarwa da yake yi ga iyalansa ba, abun takaici ma har da jariri a cikin iyalansa dan wata uku.
Idan ma bai yi tunanin lafiyar al’ummar da suke kewaye da shi ba.
“Wata matsalar ma, dakin da yake samar da wadannan miyagun kwayoyin kusa da dakin da suke dafa abinci ne, a yayin da abubuwan da aka kammala amfani da su aka sanya su a bututu kai-tsaye da suke shiga ramin tara najasar gidan baki daya, dubi wannan kasada da sayar da rai har da makwabtansa.
“A matsaikacin lissafi kamfanin yana samar da kilo 50 na Mkpuru Mmiri a kowacce mako, wanda yake da shirin kara abubuwan da yake samarwa zuwa kilo 100 a kowacce mako.
Ta ina za a iya kawo karshen ta’ammuli da miyagun kwayoyi?
“A lokacin da kuka lura da cewa farashin da ake sayar da muyagan kwaya ta Mkpuru Mmiri ya yi tsada matuka har kowacce kilo ana sayar da ita dala dubu 500 a kasuwannin duniya a kwanan nan, za ku fahimci cewa akwai dalilin da ya sanya Nzewi ya sanya rayuwar iyalansa da sauran jama’a a cikin hatsari ta hanyar samar da wannan kwaya.
“Muna kiran al’umma su kasance masu sanya idanu ga abubuwan da suke faruwa a wuraren da suke. A sanya idanu domin duk masu samar da ireiren muyagan kwayoyin nan musamma ma Mkpuru Mmiri suna nan cikin al’umma kuma inda suke samarwa ma a cikin al’umma suke kamar yadda aka samu a rukunin gidajen da ke Lekki cikin Jihar Legas. Ya kuma kamata masu lura da rukunan gidaje a rika kokarin sanya dokoki tare da sanya idanu kan gudanar da ayyukan irin haka.
“Abu ne mai kyau kowa ya san irin illar da sinadarai suke da lafiyar muhalli da kuma mutane.
Kuma mutane su rika kai rahoton abubuwa masu kama da haka da ba su aminta da su da don kuwa su ne za a cutar musamman ga lafiyarsu. Irin wadannan sinadarai suna haifar da ciwuka da makantansu.”
A cewarsa, babban abun takaici shi ne, masu wannan aikin ba sa fara aikinsu sai tsakiyar dare kamar misalin 11 na dare zuwa karfe 4 na asubahi, hakan ne ya sanya al’ummar da suke zaune a rukunin gidajen ma suka kai rahotonsu, aka dau lokaci ana bincike kafin a iya gano abun da suke yi tare da kama su.
Daga karshe, Shugaban hukumar ta NDLEA ya yaba wa kokarin jami’ansa ta yadda suka nuna gwaninta tare da gudanar da aikinsu cikin tsari.