Fadar shugaban Nijeriya ta ce bayan fara aikin matatar mai na Fatakwal a ranar Talata, kimanin manyan motocin tireloli 200 za su dunga lodin mai a matatan man ta gwamnati.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Sunday Dare, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Tuwita ranar Talata.
Hakan na zuwa ne a yayin da kamfanin mai na Nijeriya ya bayyana cewa matatar man Fatakwal ta fara aikin sarrafa danyen mai.
Da yake magana kan lamarin, Dare ya ce, “ana sa ran manyan motocin tireloli guda 200 za su rika lodin man fetur a kullum daga matatar mai, wannan na cikin ajandar gwamnatin Shuagaban kasa Bola Tinubu na sake saban fata ga Nijeriya.”
Ya kara da cewa matatar mai ta Fatakwal tana da bangarori guda biyu.
“Tsohuwar matatar mai ta fara aiki ne a yau tare da ikon tace ganga 60,000 a kowace rana na danyen mai.”