Abu na gaba da zan kuma tattaunawa a nan shi ne shin ko wadannan kananan sana’oin da ‘yan Nijeriya suke yi suna biya musu bukatunsu? A nan zan ce eh, suna biya musu sai dai kawai ba kamar yadda ake so ba.
Musamman yanzu da abubuwa suka yi tsada saboda matasalar tashin kayyakin yau da kullum. Wannan kuwa dalilai ne masu yawan gaske da suka jawo wannan tsadar tun da ba wai kawai Nijeriya ba ce take fama da wannan matasalar har da sauran kasashen duniya.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Yara 3, Sun Bukaci Kudin Fansa Naira Miliyan 100 A Jihar Kogi
- Wasu Gwamnatocin Kasashe Sun Nanata Matsayinsu Na Tsaiwa Tsayin Daka Kan Manufar Kasancewar Kasar Sin Daya Tak A Duniya
Wane abu ne mai karamar sana’a ya dace ya yi a irin wannan lokaci na tsadar rayuwa da tsadar kaya? Abin da ya kamata mai karamar sana’a ya yi a wannan lokaci shi ne: Na daya, ya san me yake samu.
Ina nufin shin kasuwancin nasa ya na bashi riba ko a’a, a nan ina so na fada wa mai karatu cewa akwai mutane da suke sana’a kullum amma ba su san me suke samu ba.
Saboda ba sa yin lissafin riba da faduwa. Shi ne ya sa sai ka ga dan kasuwa lokaci guda ya karye ya rasa menene dalili, dalilin kuwa shi ne, shi da kansa ne ya cinye duk ribar da yake samu a kasuwancinsa.
Saboda haka ya zama dole mai sana’a ya rika rubuta abin da yake samu a kullum.
Sannan kuma ya rika sanin kullum idan ya tashi daga kasuwa me ya samu riba ko akasin haka. Duk dan kasuwa ba sai a fada masa yadda ya kamata ya yi lissafin ba domin ya sani.
Saboda haka abu ne mai kyau mai karamar sana’a ya san me yake samu kullum ta hake ne yake da ma’auni a hannunsa yadda kullum zai rika auna kasuwancinsa.
Sannan abu na biyu shi ne dan kasuwa ya san inda kasuwacinsa yake so ya kai shi.
A nan ina nufin duk wani mai yin sana’a ya rubuta a takarda manufofinsa da abin da yake so ya cimma a karshe.
Misali, mutum zai shiga kasuwanci ya ce yana so ya tara miliyan goma a shekara biyu ko uku. A nan dan kasuwa shi ne zai zayyana hanyoyin da zai bi ya tara kudin.
Sannan kuma ya rinka bin duk wannan ka’idojin da manufofin da ya rubuta. Ana so duk dan kasuwa komai kankantar jarinsa ya kasance ya na da manufa da burin inda yake so kasuwancinsa ya kai shi.
Akwai kamfanoni da yawa a kasashen duniya da suka fara da kadan-kadan amma saboda sun yi tsari mai kyau da zayyana inda kasuwancinsu suke so ya je a shekarun da mutum ya tsara za’a ga wannan kamfanin ya kai.
Har ila yau, duk dan kasuwa ya sani cewa makomar kasuwancinsa tana hannunsa, a nan shi ne mai ruwa da tsaki ko mai wuka da nama ta komai na kasuwancinsa.
Shi ne ya sa dole dan kasuwa ya yarda da kasuwancin da yake. Saboda yawancin ‘yan kasuwa suna yin kasuwanci amma ba sa son kasuwacin a ransu, shi ne dalilin da ya sa sai mutum ya ga kasuwancin nasa bai kai shi ko ina ba.
Dole ne mutum ya yarda da abin da yake kada a tambaye ka ka ce ‘to gamu nan dai wannan kasuwancin dai muna yinsa ne kawai’. Kada dan kasuwa ya rinka fadar haka saboda yana nuna bai yarda da kasuwancin ba, shima kuwa kasuwancin ba zai yarda da shi ba.
Abu na ga ba shi ne, duk mai karamar sana’a ya saka a ransa cewa wannan sana’ar ita ce rayuwarsa. A nan ina nufin sana’arka ta zamanto maka ita ce abokiyar rayuwa, yadda idan wani abu ya same ta ya sami rayuwarka.
Ta ya ya za’a mayar da kasuwanci ya koma abokin rayuwa?, hanya daya ce tak.
Ka yarda a ranka cewa idan babu ita babu kai. In dai ka yi haka to hakika kasuwancinka zai kai ka inda kake so musamman idan ka tsara manufofin masu inganci da kuma yiwuwa. Kada ka kirkiri abin da ba zai yiwu ba. Kada ka zauna ka rubuta ka ce kana a kwana dari sana’arka ta tara maka Naira miliyan Dubu, idan ka yi haka to ka fara tambayar kanka nawa ne jarin da ka zuba da zai kawo maka Naira Biliyan dubu?
Wannan shi ne burin da ake cewa ba zai yiwu ba. A koda yaushe ka gina kasuwancinka a kan gaskiya da amana, saboda wadannan abunbuwan guda biyu su ne tushen ci gaban duk wani kasuwanci da mutum ya sa a ransa zai fara. Sannan abu na karshe mai son yayi kasuwanci, kada ka ko ki taba shiga kasuwancin da ba ka ko ki da ilimi a kai.
Wannan shi ne babban kuskuren da mutane suke yi a yanzu na shiga kasuwancin da ba su da ilimi a kansa. Allah Ya kiyaye.