Matakan kariyar cinikayya daga wasu kasashe masu ci gaba wadanda ke cin karo da yunkurin dunkulewar tattalin arzikin duniya ba su taba sanyaya gwiwar kasar Sin wajen kara karfafa huldar cinikayya tsakaninta da kasashe masu huldar diflomasiyya da ita ba. Daga cikin matakan baya bayan nan da kasar Sin ta dauka wajen dunkulewar tattalin arzikin duniya shi ne kasashe masu karamin karfi da ke da huldar diflomasiyya da ita za su ci gajiyar soke haraji kan kayayyakin da suke fitarwa zuwa kasar Sin. Wannan matakin ya nuna aniyar kasar Sin na tabbatar da ra’ayin bangarori daban daban, da goyon bayan cinikayya mara shinge a cikin yanayin kasa da kasa mai sarkakiya, da kuma sauke nauyin da ke wuyanta a matsayinta na babbar kasa.
Kana kasancewar kasar Sin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki, kuma kasa mafi karfi da girma a fannin cinikayyar kayayyaki, shawarwarin tattalin arziki da manufofinta na cinikayya suna da tasiri mai matukar muhimmanci. Duk da yanayin da ake ciki na yaki da kariyar cinikayya a duniya, kasar Sin ta ci gaba da bude kofa ga kasashen duniya, da ci gaba da aiwatar da matakai da shawarwarin bangarori daban daban kan yin ciniki cikin ‘yanci, da ci gaba da ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya. Wannan ba wai kawai yana taimakawa wajen tabbatar da cinikayya cikin lumana da kyautata tafiyar da tsarin masana’antun duniya da tsarin samar da kayayyaki ba, har ma yana samar da damammakin kasuwanci ga kamfanoni daga kasashe daban daban da kuma samar da mafi kyawun kason albarkatun duniya. Bugu da kari, A matsayinta na kasa mai tasowa, kasar Sin ta fahimci wahalhalun dake tattare da yunkurin neman ci gaba, kuma a ko da yaushe tana amfani da sanin ya kamata, tare da kokarin samun ci gaba kafada da kafada da sauran kasashe masu tasowa.
Muna iya ganin yadda habakar shingen kasuwanci ya sa yanayin kasuwancin duniya cikin tangal tangal, kuma bunkasar tattalin arzikin duniya na fuskantar babban matsi, don haka manufar soke haraji kan kayayyakin kasashe mara sa karfi dake shigowa kasar Sin ta ingiza fatar farfadowar tattalin arzikin duniya. Kuma ko shakka babu kasar Sin za ta ci gaba da bin hanyar samun ci gaba ba tare da wata matsala ba, tare da yin aiki da kasashen duniya don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, da ba da gudummawa sosai wajen bunkasa tattalin arzikin duniya, da tabbatar da burin ci gaban bil Adama ta bai daya. Da fatan sauran kasashe za su bi sahun kasar Sin, da daukar matakan turjewa kariyar cinikayya, da kuma tafiyar da tattalin arzikin duniya zuwa ga samun ingantacciyar alkibla mai dorewa. (Mohammed Baba Yahaya)