Mataimakin wakilin kujerar dindindin ta kasar Sin dake MDD Geng Shuang ya gabatarwa mataimakin rikon kwarya na babban sakataren majalisar Stephen Mathias “sanarwar tabbatar da shatar yankin teku na Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin da taswirarsa a tsibirin Huangyan” a jiya Litinin a madadin gwamnatin kasar Sin. Majalisar za ta saka wannan sanarwa da taswirar a shafinta na yanar gizo.
Ko shakka babu, tsibirin Huangyan yankin kasar Sin ne tun fil’azal ba yanzu ba kawai. A ranar 10 ga watan Nuwamban da ya gabata, gwamnatin Sin ta tsayar da kuma gabatar da shatar yankin teku dake kewayen tsibirin Huangyan bisa yarjejeniyar dokar teku ta MDD da dai sauran dokokin kasa da kasa da kuma dokar yankin teku da yankuna masu nasaba da Sin take da ikon mallaka da gudanar da harkokinta a ciki. Halattaccen matakin da Sin ta dauka wajen kara karfin daidaita harkokinta na teku, ya dace da doka da matakan da kasashen duniya kan dauka idan irin haka ta taso.
Bisa yarjejeniyar dokar tekun MDD, kasashen dake dab da teku dole ne su gabatarwa babban sakataren MDD shatar yankin tekunsu da taswira. Sanarwar da Sin ta gabatar a wannan karo, mataki ne da ya tabbatar da yarjejeniyar kamar yadda kasashen da suka amince da ita suka rattaba hannu a kai, kuma matakin da ya dace wajen tabbatar da cikakken yankinta da moriyarta a teku. (Amina Xu)