Tsohon kamfanin jiragen sama na Nijeriya mai zaman kansa, ‘Aero Contractors’ ya zabge farashin jirgin a tafiye-tafiyen cikin gida a lokutan gudanar da bukukuwan Kirismeti da karkashin shekara.
Kamfanin jirgin ya ce, fasinjojin za su biya Naira 80,000 zuwa duk inda za su matukar ya yi dai-dai da inda kamfanin ke zirga-zirgarsa a fadin Nijeriya.
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata, manajan daraktan kamfanin ‘Aero Contractors’, Kaftin Ado Sanusi, ya ce, tallafin wanda zai ci gaba da aiki har zuwa watan Janairun 2025, wani yunkuri ne na mayar da biki da kuma tallafawa abokan huldarsa a yayin da suke ttafiye-tafiye a lokutan hutu.