Gwamnatin tarayya ta bayyana kwarin gwiwar cewa, shirin samar da ayyukan yi ga matasa (NIYEEDEP) na tsawon watanni 24, zai samar da ayyukan yi ga matasa miliyan 20.
NIYEEDEP, shiri ne da aka kaddamar kwanan nan don tallafa wa matasa kan harkokin tattalin arziki tare da hadin gwiwar Ma’aikatar kula da raya Matasa ta Tarayya da Majalisar Dattawan Nijeriya, a karkashin kwamitinta na bunkasa wasanni.
- Mutane Biyu Sun Mutu A Wani Hatsarin Babbar Mota A Bauchi
- Xi Ya Ce Sin Ta Dukafa Wajen Ganin Duniya Na Amfana Da Magungunan Gargajiya Yadda Ya Kamata
An bayyana cewa, shirin zai samar da guraben ayyukan yi miliyan 20 ga matasa ta hanyar kawo sauyi a bangaren kasuwanci, musamman a aikin gona, da kasuwancin kayayyakin gona, fasaha, nishadantarwa da makamashi da dai sauransu, wanda aka kirkiro don samar da matasa manoma miliyan 12 a cikin watanni 24.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Litinin yayin bikin kaddamar da shirin ‘NIYEEDEP’, Ministan matasa, Ayodele Olawande, ya jaddada bukatar matasan Nijeriya su goyi bayan gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
Ya kara da cewa, ya san matasa na cikin mawuyacin hali amma ya bayar da shawara cewa, mafita daya tilo daga cikin matsalolin tattalin arzikin da ake ciki, ita ce matasa su shiga hanyoyin da suka da ce na habaka tattalin arziki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp