A bisa kokarin darawa a kan nasarar da aka samu a fanin fitar da kaya zuwa ketare, mahukunta a hukumar tashoshin Jiragen ruwa ta kasa, (NPA) sun bayar da tabbacin bayar da goyon bayan da ya kamata domin tashar Jiragen ruwa ta Burutu da ke a jihar Drlta ta samu dmar gudanar da ayyukanta yadda suka kamata
Shugaban hukumar Dakta Abubakar Dantsoho, ne ya bayar da wannan tabbacin, Abukakar ya bayar da tabbacin ne, a yayin da ya karbi bakuncin shugaba da manyan mahukuntan kamfanin Akewa Colmar Terminal Limited (ACTL), a shalkwtar hukumar da ke a jihar Legas.
- Ali Nuhu Ya Zama Jakadan Kamfanin Tsaftace Haƙora A Arewacin Nijeriya
- Gwamnoni Sun Miƙa Ta’aziyya Ga Waɗanda Wani Abu Ya Fashe Da Su A Mota A Zamfara
A lokacin ganawar Abubakar ya zama wajbi hukumar ta kara kaimi wajen zuba hannun jari mai dimbin yawa a tashoshin Jiragen rawan kasar nan.
A cewarsa, “ Na fadi hakan ne, duba da yadda aka samu nasara wajen bunkasar da aka iya gani tashoshin Jiragen sama a duniya da ked aura da iyakokin ruwa na yamma da na Afirka ta tsakiya”.
Shugaban ya kara da cewa, “ Muna kan yin aiki tukuru domin gyran hanyar ruwa ta garin Warri”.
Ya ci gaba da cewa, “ Mun shirya tsaf domin samun nasara a kan wannan aikin, da zarar tawagar kwarrun da ke aikin, sun mika rahoton su, nan da mao biyu masu zuwa”.
Tashar ta Burutu wacce ta kasance a karshen Kogin Riba Neja ta kuma hadu da sauran tashohin Jiragen ruwa na Biniwe.
An kaddamar da ita ne a 1887, a matsayin tsahar Jirgin ruwa ta farko a nahiyar Afirka ta kuma kasance a wancan lokacin, a matsayin tashar da turwan mulin mallaka ke amfani da ita, wajen yin kasuwancin kaya a tsakin Nijeriya da kasar Birtaniya.
Tasahar ta kasance bata yin wani aiki bayan yakin basa, amma daga baya, NPA domin ta sake dawo da kimar tashar, ta bayar da umarnin da a samarwa da tashar kayan aiki, bniyo bayan amincewar da majalisar zartarwa ta yi a 2023.