A yau Juma’a ne cibiyar nazarin ci gaban ilimin bunkasar kasa da kasa ta kasar Sin, ta fitar da rahoton ci gaban duniya na shekarar nan ta 2024 a birnin Beijing. Wannan wani muhimmin mataki ne ga kasar Sin na aiwatar da shirin bunkasa duniya. Kuma ya zuwa yanzu, an fitar da matakai 3 a jere masu nasaba da cimma burin hakan.
Masana da kwararrun malamai daga cikin kasar Sin da na ketare da suka yi hadakar hada rahoton, sun ce ya tattare abubuwa da dama, masu nuni ga irin tarin kalubale dake fuskantar duniya a yau, ya kuma gabatar da dabarun magancewa, don gina al’ummar duniya mai ci gaba, da gaggauta aiwatar da ajandar MDD ta ci gaba mai dorewa nan zuwa shekarar 2030. (Mai fassara: Saminu Alhassan)