Rundunar ‘yan sandan kasar Sin na ci gaba da tallafawa, da shiga a dama da ita a ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, inda daga shekara ta 2000 zuwa yanzu, ta aike da jami’anta sama da 2,700, domin halartar ayyukan wanzar da zaman lafiya 18 na MDD, da helkwatar majalissar, ciki har da ayyukan da aka gudanar karkashin tawagogin ‘yan sandan kwantar da tarzoma 13, da jami’ai sama da 1,900 da aka aike kasashen Haiti da Liberia, domin ayyukan wanzar da zaman lafiya.
Manema labarai daga kafar CMG, sun samu bayanan hakan, yayin wani taron fayyace tasirin aikin ‘yan sandan na Sin, karkashin rundunar MDD ta ‘yan sandan kwantar da tarzoma, wanda ma’aikatar lura da tsaron al’umma ta kasar Sin ta shirya.
Bayanan sun nuna cewa, jami’an MDD, da wakilai masu ruwa da tsaki a wannan aiki, sun jinjinawa ingancin aikin ‘yan sandan na Sin, da kayan aikinsu, da sanin makamar aiki. Kaza lika, sun bayyana fatan su na ganin ‘yan sandan na Sin sun kara samar da gudummawa ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)