Ta yaya ne gwamnati za ta fahimci adadin makarantu, ajujuwa da sauran kayan aikin karatu da garin ake da bukata sama da garin B?.
Hatta adadin dalibai wadanda kanana da manyan makarantunmu ya kamata su dauka a duk Shekara, na da alaka ta kud da kud, da sanin hakikanin adadin yawan jama’ar kasa.
- Kafofin Yada Labarai Fiye Da 2600 A Duk Fadin Duniya Za Su Yada Shagalin Murnar Bikin Bazara Da CMG Zai Gabatar
- Wani Abu Ya Sake Fashewa A Zamfara
Ba ya ga sanin adadin yawan dalibai da ya kamata makarantun su dauka, wajibi ne ma gwamnati ta kwana da sanin adadin wadanda ba sa zuwa makarantar.
Yayin da gwamnati ke da cikakken adadin yawan wadanda ba sa zuwa karatu, a duk sa’adda za ta bijiro da wata manufa, ta mayar da yara makaranta, idan ba ta da hakikanin adadin yawansu, tabbas wannan shiri na gwamnati zai zamto makahon shiri ne!
Rashin sanin hakikanin adadin jama’ar Nijeriya a yau, ya taimaka ainun, wajen rashin samun nasarar aikace-aikace da sauran wasu manufofi da gwamnatoci a matakai iri daban-daban suka sanya a gaba. An wayi gari, kowace makaranta na yin kintacen abinda za ta iya dauka ne, a duk karshen Shekarar daukar sabbin dalibai. Hatta ita kanta gwamnati, da tana da cikakken adadin yawan jama’ar Kasa a hannu cifcif, tana iya sanya-baki ga makarantunmu, wajen hakkake adadin wadanda ya kamata a dauka sabon zangon karatu. Yanzu haka a yau, gwamnatin taraiyar Nijeriya, jihohi hada da kananan hukumomi, ba su da wani cikakken bayanai da za su iya hakkake musu adadin yawan al’umar Kasa. Duk wasu abubuwa da za su gudanar, wadanda ke da jibi da muhimmancin sanin adadin yawan jama’a, sai dai su yi kintace ne kurum. Ko dai su gina lissafinsu ne bisa lissafin wasu hukumomi na Duniya, irin su “United Nations”, “WHO”, “UNICEF” da sauransu. Koko ma su gina lissafin nasu a kan tubalin sakamakon kidayar jama’a ta karshe da aka yi a wannan kasa, Shekaru goma sha-takwas (18) da suka gabata, 200b.
Sanin adadin malaman makaranta da za a kai makarantu, koko wata makaranta, dole yana da alaka da sanin hakikanin adadin dalibai da wannan makaranta za ta dauka, ko take da su, a matsayin dalibai. Bugu da kari, su kansu adadin ajujuwa da gwamnati za ta samar, suma suna da alaka ta kusa, da wajibcin sanin adadin dalibai da za a dauka. Sannan, idan makarantun na kwana ne, suma, suna da muradin sanin iya adadin daliban da makarantar za ta dauka a matsayin dalibai, don sanin adadin dakunan kwanan dalibai da za a samar. Mai karatu ya sani cewa, duka wadannan lissafe-lissafen adadi da ake ta faman gabatarwa, ba za a yi su cikin nasara kuma a ilmance ba, dole ne sai an fahimci hakikanin adadin yawan jama’ar kasa, wanda sanin adadin yawan jama’ar kasa kuwa, ya dogara ne kacokan a kan gudanar da aikin kidayar jama’a ta kasa baki daya akai akai (duk bayan Shekaru 10).
Duk wani shiri, ko wata manufa “policy” da gwamnatin karamar hukuma, ko jiha, koko ta tarayya za ta kirkira game da inganta fannin na ilimi, zai zamto gungun shiri ne, muddin gwamnati ta saba lambar sanin hakikanin adadin yawan jama’arta!. Ke nan, ita kanta wata sabuwar manufa, ko wani sabon shiri na gwamnati game da bunkasar ilimi, na da matukar bukatar son sanin hakikanin adadin yawan jama’ar kasa ko waje, don kaucewa, kamfa, ko daban-kwalo, tare da samun cikakkiyar nasarar da aka nufata.
Duk kasar ta gaza sanin adadin yawan mutanenta, labudda a yi ta faganniya cikin duk wani abu muhimmi da gwamnatin kasar ta sanya a gaba, ba ya ga sabgar ilimi. Akwai misalai bila-haddin, sai dai wajibi ne a takaita.
Kidayar Jama’a Da Harkar Tsaron Kasa
Tamkar irin yadda hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta bukaci duk likita guda, ya jibinci duba marasa lafiya dari shida (1:b00) a karkashisa, haka ma a bangaren na tsaro, majalisar dinkin Duniya ta nemi duk wani jami’in tsaro (dan sanda) guda, zai rika bibiyar lamuran akalla mutane dari hudu da hamsin (police-to-citizen ratio, 1:450) ne. Ta yaya ne za a iya faiyacewa tare da dabbaka wannan ka’ida, ba tare da sanin hakikanin adadin yawan jama’ar Kasa ba?. Faro tun daga daukar sabbin jami’an tsaron, sai an san yawan adadin yawan jama’ar Kasa, daga nan ne ma za a dora sanin hakikanin adadin yawan jami’an tsaron da za su wadaci Kasa aiki. Maimakon jami’i guda jama’a 450, yanzu haka a Nijeriya, duk jami’in tsaro guda, an dora masa alhakin kulawa da mutum dari shida (1:b00) ne.
Saboda rashin aza abu bisa turbarsa ne a yau a Nijeriya, Shekara da Shekaru an rasa iya dibar hakikanin adadin jami’an tsaron da ake da bukata, don kawo zaman lafiya a Kasa. Babban sifeton “yan sandan wannan Kasa, Kayode Egbetokun, da kansa ya labarta cewa, wannan Kasa tamu a yau, na bukatar karin adadin jami’an tsaro har kimanin dubu dari da casa’in (190,000). Tun da harkar daukar sabbin jami’an tsaron ta zamto canki-in-canka ne, kowane shugaba ya zo, sai dai ya kwashi adadin mutanen da ya ga dama ne, ko da yake da muradi. Ko sun wadatar, ko ba su wadatar ba oho!. Irin wannan dalili na rashin dibar jami’an tsaron wadatattu, ba karamin miki ne zai yi wa sabgar tsaron kasa ba.
Da kasar tana da hakikanin adadin yawan jama’arta, babu wata wahalarwa, ko wani aikin baban-giwa da za a yi, a duk lokacin da bukatar daukar jami’an tsaron ta zo, nan take ne za a fahimci adadin yawan da sune za su cika waccan ka’ida da majalisar dinkin Duniya ta aje, wajen tabbatar da adadin yawan jami’an tsaro, bisa la’akari da adadin yawan jama’ar kasa. A fili ne yake cewa, da yawa daga Kasashen da suke dabbaka irin wadancan ka’idoji na hukumomin Duniya, ta hanyar mayar da hankali bisa gudanar da aikin kidayar jama’a a wurarensu, sun kere Nijeriya ci gaba ta fuskoki da dama. Harkar lafiyarsu, iliminsu, tattalin arzikinsu da tsaronsu, duka sun yi wa Nijeriya shal!.
Ba wai daukar adadin yawan jami’an tsaron ne kawai kan taimaka wajen dakile ta’adar ta’addanci ba, hatta sanin adadin yawan jama’ar wuri, banbance-banbancensu, sanin hanyoyin samunsu, Shekarunsu da sauransu, kan taimaka wajen sanin duk wasu bakin-hauren da za su shigo cikin Kasa da wata boyaiyar manufa maras kyawo. Rashin sanin hakikanin jama’ar Karkara, tare da sama musu ababen more rayuwa, na daga dalilan da ke sanya su fantsama cikin birane, wanda a karshe ake kaiwa ga cunkushewa wuri guda. Duka wadannan ababen ki a kan magance afkuwarsu ne ta fuskar gudanar da sahihiyar kidayar jama’a a kasa.
Hatta a bangaren samun ci gaban tattalin arzikin Kasa, sanin hakikanin adadin yawan jama’ar kasa, kan taimaka wajen samun ababen more rayuwa masu tarin yawa daga gwamnati. Ta yaya ne jiha kamar Kano da ta kusan ninka jihar Nassarawa har kimanin sau hudu, za a gabatar musu da ababen more rayuwa adadi iri guda?. Idan jihar Nassarawa na da bukatar a sama mata da megawat na wutar lantarki dari biyar ne. Ke nan, jihar Kano na da bukatar a kai mata megawat na wuta dubu biyu ne. Mai yi wa, irin wannan dalili ne ma ya sa a lokacin jamhuriyar siyasa ta biyu (2nd Republic, 19b0 – 19bb) ake raba arzikin Kasa ga jama’ar kasa, bisa la’akari da yawan mutane da kowace jiha a kasar take da. Bugu da kari, shi sanin adadin yawan mutane da wata jiha ke da shi, ba ita kadai ce za ta amfanu da hakan ba, hatta gwamnatoci ma za su amfana, ta hanyar sake fasalta tsarin samun kudadenta na shiga a irin wadannan wurare dake dauke da jama’a jingim. Haka ma masu cutar yatsun hannu, ko na rashin gani da sauransu, adadinsu kan banbanta daga waje ne zuwa waje, saboda haka, bayar da tallafi iri guda ga daukacin jihohi 3b na Kasar, hada da Abuja, zai zamto tamkar wani rashin adalci ne. Ke nan, gudanar da kidayar, zai zamto hatta masu bukata ta musamman ma za su shana ne, ma’ana, za su kurbi romon dauki daga gwamnatocin gida da na waje, sama da irin yadda suke samu a yau.
Mabanbantan aji-aji na mutane, misali masu bukata ta musamman, kan mori agaji daga Kasa da kuma sauran kasashen ketare, yayin da aka san hakikanin adadinsu a wuri. Za a san adadin nasu ne ta hanyar gudanar da kidayar jama’a a Kasa.
Daga Kalubalen Da Ke Fuskantar Sha’anin Kidaya A Nijeriya
Tun daga lokacin Turawan Birtaniya da suka mulki wannan Kasa, kuma suka fara gudanar da aikin kidayar jama’a zuwa yau, kowane lokaci aka yunkura aiwatar da kidayar, akan yi kwalli, ko ci-karo ne da mabanbantan matsaloli, wadanda wasu mabanbantan dalilai da mabanbantan rukunonin mutane ke haifar da su. Ga wasu daga matsaloli da tsarmakatan kamar haka;
1- Daga kalubalen kidayar a lokacin Bature, shi ne, an fara gudanar da aikin kidayar ne kawai a yankin Lagos, maimakon a Kasa bakidaya.
2- Akwai karancin kudi, da kanfar kwararru masana, wadanda za su gudanar da aikin kidayar, tun a lokacin “yan mulkin mallakar.
3- Turawan, sun fi mayar da hankali ne wajen sanin romon harajin da za su amsa daga jama’ar gari ne, maimakon yunkurin bunkasar rayuwar jama’a, wanda ya hadar da iliminsu, tsaronsu, tattalin arzikinsu da sauransu, ta hanyar dabbaka gudanar da aikin kidayar.
4- Bayan amsar “yancin-kai, mummunar wutar kabilanci da ta rika ruruwa a tsakanin mabanbantan larduna uku na kasar, da mabanbantan kabilun Kasar, sune kan gaba wajen kawo cikas cikin batun kidayar a kasa.
5- Dalilan siyasa ma sun taimaka wajen kawo tarnaki ga sabgar kidayar.
b- Rashin fahimta ta addini, da kuma wasu al’adu, sun kasance daga tarnakin da sha’anin kidayar jama’ar ke fuskanta a Nijeriya.
7- Wasu daga manyan jami’an kidayar, hada da malaman kidayar, kan shigar da son zuciya cikin aikin kidayar, musamman wajen hada-baki da wasu daga jami’an gwamnati, don yin karin-gishiri yayin fitar da sakamakon kidayar.
8- Rashin dabbaka wasu hanyoyi na zamani yadda ya kamata, don yaukaka, kyautata tare inganta aikin kidayar jama’ar a Kasa cikin sauki.
9- Jahilci rawanin tsiya, shi ma kan taka rawa wajen kassara sabgar ta kidaya.
10- Gwamnatoci, kan yi zagon-kasa cikin lamarin kidayar.
11- Karayar tattalin arzikin Kasa ma kan yi wa harkar turkoko.
12- “Yan-ta’adda da ta’addanci, kan kawowa zarafin kidayar cikas.
Wadannan ne wasu daga cikin manyan ababen dake kawowa sabgar kidayar jama’a tarnaki a wannan kasa, sama da Shekaru 100 da suka gabata. Kawo karshen matsalar, zai zamana, samar da kishiyoyin abubuwan da aka lasafta, shi ne waraka. Misali, “jahilci rawanin tsiya”, sai ya zamana cewa, gwamnatin taraiya, gwamnatin jiha da ta karamar hukuma, su dukufa fadakarwa tare wayarwa da jama’a kai, wajen fahimtar alfanun kidayar, ko ba komai, sai matakin ya kawar da jahilcin da yai musu katutu.