Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), ta bayyana shekarar 2024 a matsayin shekarar da ta fi fuskantar kalubale ga ma’aikata a kasar.
Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja a wani taron Makarantar Harmattan ta 2024, mai taken “Kungiyoyin Kasuwanci da Neman Sabuwar Kwangila ta Zamantakewa.”
- UNESCO Ta Sanya Karin Al’adun Gargajiya 3 Cikin Jerinta Na Al’adun Gargajiya Da Ba Na Kayayyaki Ba
- Sin Ta Aike Da ‘Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma Sama Da 2,700 Daga Shekarar 2000
A cewarsa, shekarar 2024 ta cika da tsananin wahala ga ma’aikata a kasar nan.
“Ina maraba tare da ku na ganin shekarar da muke ciki wadda muka shaida daya daga cikin mafi girman tashin hankali a tarihinmu na masu gwagwarmaya. Lokaci ne da aka kai ta mana yaudara, an kuma yi mana barazana da tsoratarwa,” in ji shi.