Jakadan kasar Sin a Tarayyar Najeriya Mista Yu Dunhai, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar, a ranar Alhamis. Yayin ganawar ta su, jami’in na kasar Sin ya ce a tsawon lokaci Sin da Najeriya sun raya huldar kut-da-kut, kuma tushen wannan hulda shi ne girmama juna, da amincewa da juna, gami da kokarin rufa wa junansu baya.
Kaza lika Yu, ya ambaci ziyarar da shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya kai kasar Sin a watan Satunban da ya wuce, tare da halartar taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC), wanda ya gudana a birnin Beijing na kasar Sin, inda shugaban tare da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, suka sanar da daga matsayin huldar kasashensu, zuwa huldar abota da ta shafi manyan tsare-tsare a dukkan fannoni.
- Shekarar 2024 Babban Kalubale Ne Ga Ma’aikatan Nijeriya – Kungiyar NLC
- An Gudanar Da Babban Taron Kirkire-Kirkiren Kimiyya Da Fasaha Na 2024 A Shanghai
Mista Yu ya kara da cewa, kasar Sin na son hadin gwiwa tare da Najeriya, a kokarin aiwatar da matsaya daya da shugabannin kasashen 2 suka cimma yayin ganawarsu, da dimbin sakamakon da aka samu a taron FOCAC da ya gudana, don kara ciyar da huldar dake tsakanin kasashen 2 gaba.
A nasa bangare, minista Tuggar ya ce, ziyarar da shugaba Bola Tinubu ya kai kasar Sin a karon da ya gabata, ta haifar da dimbin nasarori, tare da daga huldar dake tsakanin Najeriya da Sin zuwa wani sabon matsayi. Kaza lika, bangaren Najeriya na son yin hadin kai tare da Sin a fannin raya manyan tsare-tsare, da sanya hadin gwiwar kasashen 2 ya samar da karin alfanu ga jama’arsu. (Bello Wang)