Tun daga farkon shekarar bana, cibiyoyin hada-hadar kudi na kasar Sin na ci gaba da fadada kwazo, wajen samar da hidimomin kudade ga sashen tattalin arziki mai nasaba da sarrafawa, da sayar da hajoji da hidimomi, kana sun kara zurfafa sauye-sauye da bude kofa.
Tun daga watan Satumba da ya gabata, hukumomin dake lura da ka’idojin hada-hadar kudade na kasar, sun gabatar da matakai na kara aiwatar da manufofi, domin ingiza cimma nasarar gina tattalin arziki da ake fata a shekarar nan baki daya.
- Jakadan Sin Ya Gana Da Ministan Wajen Najeriya
- Sin Ta Aike Da ‘Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma Sama Da 2,700 Daga Shekarar 2000
Bugu da kari, Sin ta himmatu wajen ingiza hade sassan kasuwannin hada-hadar kudade, da kyautata samar da muhallin musayar jarin waje na kai tsaye. Inda aka fitar da wasu manufofi domin cimma nasarar hakan, yayin da kuma kasar ke kara zurfafa aiwatar da manufar bude kofa bisa matsayin koli, a bangaren sassa dake hada-hadar kudade.
Har ila yau, a bangaren kasuwar takardun lamuni, kasar Sin tana aiwatar da wasu jerin tsare-tsaren hukuma, don samar da hanyoyi daban-daban na fadada zuba jari, da bude hanyoyin shigar da karin kudade cikin kasuwannin hada-hadar kudi na duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)