Yau Litinin, a Bejing, fadar mulkin kasar Sin, firaministan kasar Li Qiang, ya yi shawarwari da ake kira “1+10” tare da shugabannin wasu muhimman kungiyoyin tattalin arziki na kasa da kasa, ciki har da shugabar sabon bankin samar da ci gaba, Dilma Rousseff, da shugaban bankin duniya, Ajay Banga, da babbar darektar hukumar cinikayya ta duniya wato WTO, madam Ngozi Okonjo-Iweala, da kuma babbar darektar asusun bada lamuni na duniya ko kuma IMF a takaice, madam Kristalina Georgieva, inda suka zurfafa tattaunawa bisa jigon “cimma matsaya kan samar da ci gaba, da raya duniya cikin hadin-gwiwa”.
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya bayyana cewa, ci gaban tattalin arzikin duniya na da rauni a halin yanzu, kuma dunkulewar tattalin arzikin duniya gami da ra’ayin kasantuwar bangarori daban-daban na fuskantar cikas da kalubale, al’amarin dake haifar da rashin tabbas da dama. Kasar Sin na son yin kokari tare da sassan kasa da kasa, don kiyaye muhimman ka’idojin dangantakar kasa da kasa, da tsarin gudanar da cinikayya dake kunshe da bangarori daban-daban, kaza lika, Sin na goyon-bayan kungiyoyin tattalin arziki na kasa da kasa da su kara taka muhimmiyar rawa wajen daidaita harkokin duniya, za kuma ta ci gaba da daukar nauyin dake rataye a wuyanta, a wani kokari na taimakawa ci gaban tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.
Su ma shugabannin manyan kungiyoyin tattalin arzikin duniya sun yaba sosai da manyan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin samar da ci gaba, inda a cewarsu, habakar tattalin arzikin Sin, da kokarin fadada bude kofarta ga kasashen waje, na sanya kuzari ga tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya. Suna kuma da yakini sosai game da sauyawar salon tattalin arzikin kasar Sin gami da makomarsa a nan gaba. (Murtala Zhang)