Ma’aikatar harkokin wajen Sin da ofishin manyan jami’ai masu kula da hakkin Bil Adama na MDD, sun shirya taron karawa juna sani kan hakkin tattalin arziki, da al’umma, da al’adu na kasa da kasa cikin hadin gwiwa a birnin Hangzhou dake gabashin kasar Sin. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gabatar da jawabi a rubuce.
A cikin jawabinsa, Wang ya ce, tabbatar da hakkin tattalin arziki, da al’umma, da al’adu na kowa, wani muhimmin aiki ne na tabbatar da hakkin Bil Adama. Kuma dole ne a nace ga gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban, da mutunta hanyoyin da duk wani sashe ke zaba wajen raya hakkin Bil Adama, da ma maida bautawa jama’a a gaban komai, da kara taka rawar gani wajen tabbatar da hakkin jama’a a wadannan bangarori 3.
Wakilai da suka kunshi ministoci, da manyan jami’ai daga kasashe ko yankuna 50 ciki har da Kongo Brazaville, da Kwadifwa da Mauritaniya, da Yemen da sauransu, da masanan MDD, da jami’an ofishin babban kwamishina mai kula da hakkin Bil Adama na MDD sun halarci taron. (Amina Xu)