Hukumar kula da kwallon kafa ta duniya, FIFA ta tabbatar da cewa, za a gudanar da gasar cin kofin kwallon kafa ta maza ta duniya ta shekarar 2034 a kasar Saudiyya, yayin da Spain, Portugal da Morocco za su karbi bakuncin gasar ta 2030 tare.
Masarautar Saudiyya ta bayyana ra’ayinta a bara a wani yanayi wanda ya sa FIFA hade zabukan karbar bakuncin kofin Duniya na shekarar 2033 da 2034 a waje daya, hukumar ta yanke wannan hukunci ne a wani zama da mahukuntan suka yi ta yanar gizo yau Laraba wanda aka wallafa a shafin X na hukumar ta FIFA.
- Hukumar Hisbah Ta Kama Fiye Da Katan 200 Na Barasa A Sokoto
- Tinubu Ne Ya Fara Amanna Da Harkar Crypto Kafin Trump – Shugaban SEC
Majalisar zartaswa ta FIFA ta kuma amince da gasar cin kofin duniya na shekarar 2030, wanda za a gudanar a kasashe shida kuma a nahiyoyi uku, inda za a gudanar da wasanni uku na farko a Argentina, Paraguay da Uruguay.
Sai dai matakin bai wa Saudiyya hakkin karbar bakuncin kofin Duniya a shekarar 2034 yana samun suka da cece-kuce sosai, inda masu sukar ke ganin cewa, ana kokarin wanke kasar ta Saudiyya daga zargin da ake mata na mulkin kama karya.
Ana sukar masarautar Saudiyya saboda yadda wasu ke daukar ta a matsayin masarautar da ke take hakkin dan Adam, da kuma haramta auren jinsi ko wani abu makamancin shi, da hana fadin albarkacin baki, da kuma rashin ‘yancin mata.
Masarautar za ta karbi bakuncin gasar kwallon kafa mafi shahara a karon farko, wanda ke nuni da yadda Saudiyya ke kara yin tasiri a harkokin wasanni a duniya.