Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, kan kuɗi Naira miliyan 500, biyo bayan tuhumar sa da ake yi na karkatar da kuɗaɗe.
Mai shari’a Emeka Nwite, ne ya bayar da belin tare da dage ci gaba da sauraren ƙarar zuwa watan Fabrairu, bayan ya saurari hujjojin lauyoyi a kan lamarin sannan ya umarci wanda ake kara da ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa waɗanda sun mallaki kadarorin da suka kai darajar kuɗin.
Alƙalin ya kuma bayar da umarnin cewa waɗanda za su tsaya masa dole ne su yi rantsuwa a takardar shaida kan karɓar belin da miƙa ta ga magatakardar kotun don tantance su.
Ya umurci Yahaya Bello, da ya miƙa fasfo ɗinsa na tafiye-tafiye kuma zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali da ke Kuje, har sai an kammala cika sharuɗɗan belin.
Tun da farko dai an gurfanar da Yahaya Bello, a gaban kotu bisa tuhume-tuhume 19 da suka haɗa da laifin karkatar da kuɗaɗe har Naira biliyan 82.