Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, a karshen mako ya gana da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a Abeokuta, jihar Ogun.
Kwankwaso ya gana da Obasanjo ne a dakin karatu na ‘Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL)’ da ke Abeokuta, tare da tsohon gwamnan jihar Kros Ribas, Donald Duke.
Tsohon gwamnan na Kano ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa a shafin sa na X (twitter).
Kwankwaso ya bayyana cewa, yayin ziyarar ban girma da ya kai, an tattauna kan “muhimman batutuwan kasa, ciki har da makomar siyasa da shugabanci a Nijeriya”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp