Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da ke tunanin rusawa ko rage matsayin Ma’aikatun yada Labarai da su sake tunani, yana mai jaddada mahimmancin su wajen hulɗa da jama’a, wayar da kai, da kuma haɗin kan al’umma.
Idris ya yi wannan kiran ne yayin taron Majalisar Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai karo na 48 a Kaduna a ranar Juma’a, mai taken “Inganta Gudanar da Yaɗa Labarai don Shugabanci Mai Haɗin Kai: Ajandar Sabunta Fata.”
- ASUU Reshen Jami’ar Sa’adu Zungur Ta Dakatar Da Yajin Aiki
- Rai Da Lafiyar Mazajenmu Ya Fi Mana Jarumtarsu
Ya ce, “A wannan lokaci, ina son yin roƙo mai matuƙar mahimmanci ga wasu daga cikin gwamnatocin jihohin mu, musamman kan matsayi da ayyukan Ma’aikatun Yaɗa Labarai na Jihohi.
“Kuma roƙo na shi ne: a shugabanci, ba za a taɓa musanta muhimmancin Ma’aikatun Labarai ba a matakin tarayya da jiha. Waɗannan Ma’aikatu sun zama wata gada tsakanin manufofin gwamnati da ‘yan ƙasa da aka tsara su amfana da su, ta yadda za su samar da gaskiya, da riƙon amana, waɗanda su ne ginshiƙan kowace dimokiraɗiyya mai ci gaba.”
Idris ya jaddada cewa Ma’aikatun Yaɗa Labarai suna da matuƙar muhimmanci wajen wayar da kan jama’a, yaƙi da labaran ƙarya, da tabbatar da isar da manufofi da shirye-shiryen gwamnati yadda ya kamata.
Ya bayyana ma’aikatar a matsayin “jigon dimokiraɗiyya da cigaba,” musamman a ƙasa mai ɗimbin bambance-bambance kamar Nijeriya.
Da yake magana akan Ajandar Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Idris ya ce wannan kira ne na shugabanci mai kawo sauyi wanda ya dogara kan haɗin kai da gaskiya.
Ya ce shugabanci ya ta’allaƙa ne ga iyawarsa na haɗawa, sadarwa, da ƙarfafa haɗin gwiwar jama’a.
Ministan ya shawarci Manajojin Watsa Labarai da su yi amfani da fasaha, ciki har da na’ura mai ƙwaƙwalwa (AI), don inganta sauri da sahihancin saƙonnin su.
Ya kuma jaddada muhimmancin muhawarar jama’a wajen gyaran manufofi, yana bada misali da tattaunawar da ake yi kan sauye-sauyen haraji da Shugaba Tinubu ya gabatar.
“A kowace dimokuraɗiyya, karfin shugabanci yana da tushe sosai a cikin ikonsa na nuna muradun jama’a. Manufofin jama’a, yayin da aka ƙera su da kyakkyawar niyya, dole ne su ci gaba da bunƙasa don biyan buƙatu da tsammanin ‘yan ƙasa,” inji Idris.
Idris ya kuma jaddada buƙatar horas da jami’an yaɗa labarai kan dabarun tabbatar da gaskiya da haɓaka haɗin gwiwa da kafofin watsa labarai don yaƙi da labaran ƙarya.
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu kwanan nan ya amince da sakin kuɗi don fara aiki da Cibiyar UNESCO ta Category-2 Media and Information Literacy (MIL), wacce za a kafa a Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (NOUN) da ke Abuja.
Ya ce, “A lokacin da labaran ƙarya, furofaganda, da rahotannin son zuciya ke iya tasiri sosai kan ra’ayin jama’a da yanke shawara, fahimtar kafofin watsa labarai yana ƙarfafa tunani mai zurfi.
“Yana taimaka wa mutane su nazarci manufar saƙonnin kafofin watsa labarai, su fahimci yanayin da aka gabatar da su, da kuma tantance sahihancin su.
“Don haka ina kira ga Kwamishinonin Yaɗa Labarai da su yi amfani da wannan cibiya mai matuƙar muhimmanci da zarar ta fara aiki domin ƙara inganta ƙwarewar ma’aikatansu wajen yaƙar labaran ƙarya,” inji shi.
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, shi ne ya buɗe taron.
Taron ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki da suka haɗa da Sanata Kenneth Eze, Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, da Hon. Olusola Steve Fatoba, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Yaɗa Labarai, Wayar da Kai, Ɗa’a, da Ɗabi’u.