’Yan sama jannati na kumbon Shenzhou-19 da ke tashar sararin samaniya ta kasar Sin, sun yi nasarar kammala ayyukansu na farko da suka fita daga cikin kumbon suka aiwatar a wajensa, da misalin karfe 9:57 na dare agogon Beijing, ranar Talata, kamar yadda Hukumar Sararin Samaniya ta kasar Sin (CMSA) ta bayyana.
’Yan sama jannatin, Cai Xuzhe, Song Lingdong da kuma Wang Haoze, sun yi aiki na tsawon sa’o’i tara domin kammala ayyuka daban-daban ciki har da kafa na’urorin kandagarkin baraguzan sararin sama. Sun gudanar da ayyukan ne bisa taimakon bangaren mutum-mutumin tashar sararin samaniyar da kuma tawagar masana da ke doron kasa.
An samu nasarar kammala ayyukan na wajen kumbon Shenzhou-19 na karon farko dari bisa dari, inda hakan ya kafa sabon tarihi game da tsawon lokacin da aka kwashe na gudanar da ayyukan wajen kumbo da ’yan sama jannatin na kasar Sin suka aiwatar, kamar yadda CMSA ta bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)