• English
  • Business News
Wednesday, September 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wakilin Sin Ya Ki Amincewa Da Zargin Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Makamashin Nukiliyar Kasar Sin

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Wakilin Sin Ya Ki Amincewa Da Zargin Da Amurka Ta Yi Kan Manufofin Makamashin Nukiliyar Kasar Sin

China's delegates are seated during the 2022 Nuclear Non-Proliferation Treaty (NPT) review conference, in the United Nations General Assembly, Monday, Aug. 1, 2022. (AP Photo/Yuki Iwamura)

Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

A halin yanzu, ana gudanar da babban taro karo na 10, na dudduba yarjejeniyar haramta yawaitar makaman nukiliya, a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York, inda a kwanan nan, wakilin kasar Amurka ya yi zargin cewa, wai kasar Sin tana gaggauta habaka makaman nukiliyarta, da kin gudanar da shawarwari tare da bangaren Amurka, kan batun takaita amfani da makaman nukiliya. 

Game da irin wannan zargi da Amurka ta yi ba gaira ba dalili, wakilin kasar Sin Ding Tongbing, ya bayyana kin amincewa. Ding ya bayyana cewa, kasar Sin bata yarda da zargin Amurka, kan manufofin Sin game da makamashin nukiliya.

  • Kasar Sin Ta Musanta Zarge-zargen Amurka Game Da Atisayen Da Take Yi A Kewayen Taiwan

A cewarsa, zargin na Amurka ba zai canja hakikanin gaskiya ba, wato a matsayinta na babbar kasa mai yawan mallakar makaman nukiliya, har yanzu, ma’ajiyar makaman nukiliyar ta na kara kawo barazana ga zaman lafiyar dukkanin duniya.

Bugu da kari, Amurka ta kara daukar wasu matakai, wadanda suka haifar da babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya.

Ding ya kara da cewa, kasar Sin ta dade da kokarin takaita mallakar makaman nukiliya, don biyan bukatun tabbatar da zaman lafiya da tsaron kan ta kadai.
Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta taba shiga takarar makaman nukiliya a lokacin baya ba, kuma ba za ta yi hakan a nan gaba ba.

Labarai Masu Nasaba

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

Ya ce makasudin kasar Sin na mallakar makaman nukiliya shi ne, hana sauran kasashe su yi amfani da na su kan kasar Sin.

Kuma muddin ba su yi amfani da makaman nukiliya kan kasar Sin ba, babu bukatar daukar nata makaman nukiliyar a matsayin barazana, kuma, ba za su ji irin wannan barazana daga kasar Sin ba. (Murtala Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

NDLEA Ta Cafke Tsohon Sojan Da Ke Wa ‘Yan Bindiga Safarar Miyagun Kwayoyi

Next Post

Naira Miliyan 5 Nake Nema Don Fansar Mahaifiyata – Mace Mai Safarar Kwayoyi

Related

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Daga Birnin Sin

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

10 hours ago
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
Daga Birnin Sin

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

11 hours ago
Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok
Daga Birnin Sin

Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

12 hours ago
Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari
Daga Birnin Sin

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

13 hours ago
Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi
Daga Birnin Sin

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

14 hours ago
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Daga Birnin Sin

Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire

16 hours ago
Next Post
Naira Miliyan 5 Nake Nema Don Fansar Mahaifiyata – Mace Mai Safarar Kwayoyi

Naira Miliyan 5 Nake Nema Don Fansar Mahaifiyata - Mace Mai Safarar Kwayoyi

LABARAI MASU NASABA

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

Sowore Ya Maka DSS, Meta da X A Kotu Kan Take Masa Haƙƙi

September 17, 2025
Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi

September 17, 2025
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo

September 16, 2025
Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani

September 16, 2025
Sauye-sauyen Manufofin Gwamnati Na Iya Hana Masu HND Zuwa NYSC

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

September 16, 2025
Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

Sin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTok

September 16, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Hutun Sati 2 A Ƙasar Faransa

September 16, 2025
Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

Sin Da Ghana Na Fadada Hadin Gwiwa A Bangaren Ciniki Da Zuba Jari

September 16, 2025
Sojoji

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

September 16, 2025
Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

Yawan Hatsin Da Aka Girbe A Kasar Sin Tsakanin Shekarar 2021-2025 Ya Kai Wani Sabon Matsayi

September 16, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.