Uwargidan shugaba Xi Jinping na kasar Sin, madam Peng Liyuan ta ziyarci dakin ajiye kayayyakin tarihi a yankin Macao na kasar Sin, bisa rakiyar Cheng SooChing, mai dakin kantoman yankin Ho Lat Seng. A ziyararta, madam Peng ta dudduba kayayyakin tarihi cikin tsanake don fahimtar sauye-sauyen da yankin Macao ya samu cikin dogon tarihinta, da cudanyar Sin da kasashen yamma a fannin gine-gine da sana’o’i da al’adu da sauransu, inda kuma ta yi mu’ammala sosai da masu gadon fasahohin gargajiya na zane-zanen kayayyakin tangaran, da sassakar ice, da dai sauran fasahohin da aka gada daga kaka da kakkani.
A bene na 3 na dakin ajiyar kayayyakin tarihin, Peng ta yi hira da yaran da suka ziyarci dakin. Inda ta kara wa yaran kwarin gwiwar kara himmar gadon nagartattun fasahohin al’adu na gargajiya na Sinawa, don karfafa kishin kasar, kana da kokarin neman ilmi da koyon fasahohi, ta yadda za su samar da gudunmowa ga aikin raya yankinsu da ma kasarsu ta Sin baki daya. (Amina Xu)