Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga kasa da kasa su saurari kiran gaggawa ta al’ummar Sudan ta neman zaman lafiya, kuma su hada hannu wajen samar da sharuddan warware batun na Sudan.
Fu Cong ya bayyana haka ne jiya Alhamis, yayin taron Kwamitin Sulhu na MDD kan batun, inda ya ce, rikicin Sudan ya shiga wata na 20, kuma har yanzu yakin na ci gaba da wakana, adadin fararen hula dake jikkata na karuwa, kuma adadin wadanda ke rasa matsugunansu ya kai wani sabon mataki. Ya ce Kwamitin Sulhu ya amince da wasu kudurori 2 game da yanayin na Sudan. Kuma abu mafi muhimmanci a yanzu shi ne, tabbatar da aiwatar da kudurorin yadda ya kamata, da yayyafawa yanayin ruwan sanyi tare da kare tsaron fararen hula.
A cewar Fu Cong, kasar Sin na fatan MDD za ta karfafa hada hannu da kungiyoyin yankin kamar Tarayyar Afrika da kungiyar raya yankin gabashin Afrika ta IGAD da kungiyar kawancen kasashen Larabawa, wajen lalubo sabbin hanyoyi kuma ingantattu da za su kai ga warware rikicin. Bugu da kari, ya ce a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen duniya wajen bayar da gudunmuwar da za ta kawo karshen yakin Sudan da wuri. (Fa’iza Mustapha)