In muka yi nazari za mu fahimci cewa haka abin yake a mafi yawa na daga cikin ma’aurata Hausawa. Yawanci dukkan ma’aurata ba su damu da bayyanar da so da kauna ga junansu ba, ta hanyar kalamai masu dadi da suka dace ba kamar; Wasanni da barkwanci, kulawa ta musamman da sauransu, ko kuma ya kasance daya daga cikin ma’aurata na kokarin bayyanar da soyayya amma daya bai nuna jin dadinsa balle har shi ma ya yi kokarin yin irin yadda ake masa.
Abubuwan da ke hana bayyanar da soyayya
Al’ada: Yanayin al’ada na taka muhimmiyyar rawa sosai wajen rashin bayyanar da soyyaya a cikin rayuwar aure, a al’adance ba wata soyayyar da ake yi da ta wuce namiji ya samar da kayan bukatun rayuwa ita kuma mace ta kula da gida da yara, kowa yadda ya tashi ya ga ana yi a gidansu, a garinsu, haka zai yi, wanda ko duk aka ga ya fita daban ta hanyar yin abubuwan nuna kauna da kulawa nan da nan za a samu wani lakabin da aka yi masa saboda hakan.
Halin mazantaka: Yanayin halayyar namiji ta sa ya fi iya nuna soyayyarsa da kulawarsa ta bangare daya kawai, shi ne ta hanyar sadaukar da dukiyarsa, lokacinsa da karfinsa ga iyalinsa, wannan kam lallai shi ya fi muhimmanci kuma ya fi amfani, amma dayan da ba su cika yi ba, shi ya fi dadi da sa kwanciyar hanKali da aminci a zuciya.
Tsoro: Wannan shine ja gaba daga cikin abubuwan da ke hana ma’aurata bayyanar da soyayya a tsakaninsu, yawanci ma’aurata maza na ganin bayyanar da soyayya, kamar bayyanar da rauninsu ne, kuma hakan zai sa matan su raina su ba su ganin kimarsu. Su kuma matan na tsoron in su cika bayyana soyayyarsu, mazan za su dauke su ba bakin komai ba, kuma ba za su samu irin kulawar da suke so ba daga gare su.
Rikon laifi: Kasawar wadansu ma’aurata ga yafe laifin da abokan aurensu suka yi musu na hana su iya bayyanar da soyayyarsu, domin rikon laifi na dakushe soyayya ko ya sumar da ita gaba daya.
Za Mu Ci Gaba Mako Mai Zuwa In Allah Ya Kai Mu