Da safiyar yau Litinin ne aka kammala aikin shimfida ramin Shengli na tsaunin Tianshan , da ya kasance rami mafi tsawo a duniya da ya ratsa ta manyan tsaunuka masu matukar kalubale.
Ramin mafi tsawo a duniya wanda ya ratsa ta tsaunukan da kankara ta mamaye a arewa maso yammacin yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa na kasar Sin, ya nuna wani gagarumin ci gaba da aka samu a fannin bunkasa ababen more rayuwa a kasar Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere).