Gwamnatin kasar Habasha ta jinjina wa kamfanin kasar Sin na Huajian Group bisa gagarumar gudummawar da ya bayar wajen zuba jari a kasar.
Gwamnatin kasar ta jinjina wa kamfanin ne a wata sanarwa da Kamfanin Bunkasa Masanaantu na Habasha mai lakabin IPDC, da ke kula da sashen samar da masanaantu da kamfanoni a kasar ya fitar, a ranar Asabar da ta gabata.
- Xi Da Shugaban Botswana Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 50 Da Kulla Alaka
- Xi Ya Jaddada Samun Nasara Na Dogon Lokaci Kan Yaki Mai Tsauri Da Cin Hanci Da Rashawa
Jamian IPDC sun ce kamfanin na kasar Sin Huajian Group, ya kirkiro da ayyukan yi wadanda dubban Habashawa ke cin moriyarsu, baya ga kokarinsa na bayar da gudummawa a fannin bunkasa kimiyya da ilimi da kuma dabarun aiki.
Daga bayanan da IPDC ya fitar, kamfanin Huajian ya zuba jarin akalla dalar Amurka miliyan 150 a kasar ta Habasha da ke gabashin Afirka, inda hakan ya samar da guraben ayyukan yi ga Habashawa fiye da 12,000.
A yayin da yake tattaunawa da wakilan kamfanin Huajian na reshen Habasha, shugaban kamfanin na IPDC Fisseha Yitagesu, ya jaddada kudirin gwamnatin Habasha na ci gaba da ba da goyon baya ga harkokin zuba jari da kamfanin yake gudanarwa a halin yanzu da kuma wadanda zai yi nan gaba a kasar ta Habasha. (Abdulrazaq Yahuza Jere)