Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayar da umarnin aiwatar da dukkanin matakan da suka wajaba, na ceton rayukan jama’ar da girgizar kasa mai karfin maki 6.8 ta aukawa, a wata gunduma ta jihar Xizang mai cin gashin kai dake kudu maso yammacin kasar da safiyar jiya Talata.
Shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin kasar Sin, ya kuma ba da umarnin kara azamar jinyar wadanda suka jikkata.
- Éric Chelle Ya Zama Sabon Kocin Super Eagles
- Yawan Lambobin Mallakar Kere-Kere Na Kasar Sin A Shekara Ta 2024 Ya Kai Miliyan 4.756
Har ila yau, ya yi kira da a zage damtse wajen dakile duk wata annoba da ka iya biyo bayan girgizar kasar, kana a tsugunar da wadanda suka rasa muhallansu yadda ya kamata, tare da kyautata ayyukan farfadowa bayan girgizar kasar.
Rahotanni na cewa ya zuwa karfe 9 na daren jiya Talata, agogon Beijing, an tabbatar da rasuwar mutane 126, da jikkatar wasu 188 sakamakon ibtila’in girgizar kasar. (Saminu Alhassan)