Rundunar ‘yansandan Nijeriya a Jihar Adamawa ta yi wa jami’anta 110 karin girma a ranar Talata.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, Morris Dankombo, ya yi wa sabbin jami’an ƙarin girma da ɗaura musu sabbin muƙamai a wani taro da ya jawo hankalin jama’a.
- NDLEA Ta Cafke Masu Ta’ammali Da Ƙwayoyi 18,500 A 1 – Marwa
- Awannin Da Sallamarsu A Matsayin Kwamishinoni, Gwamnan Bauchi Ya Naɗa 3 A Matsayin Mashawarta
Bugu da ƙari, Kwamishinan ya yi wa mataimakan Sufiritandan ‘yansanda 84 ado da sabbin muƙamansu na Mataimakin Sufiritandan ‘yansanda (DSPs).
A jawabinsa, CP Morris Dankombo, ya taya jami’an murna da kuma jan hankalinsu da su ci gaba da jajircewa, sadaukar da kai, da kuma nuna ƙwazo wajen aikinsu.
Ya kuma yi kira ga jami’an da suka samu ƙarin girma da su kara ƙoƙari wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Adamawa.
A madadin waɗanda aka yi wa ƙarin girma, jami’in ‘yansanda DPO na Numan, CSP Alfred Futuwe, ya miƙa godiyarsa ga Sufeto Janar na ‘yansanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, da hukumar ‘yansanda da kuma sauran hukumomin da suka taimaka.
Taron ya samu halartar manyan baki ciki har da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Yola ta Arewa, shugabar alƙalin alƙalan jiha, shuwagabannin ƙananan hukumomi, sarakunan gargajiya, malamai, da sauran jami’an tsaro da abokan arziƙi.