Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana a ranar Talata cewa, kasar Sin za ta yi aiki tare da kasashen Afirka wajen aiwatar da shirin samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba wato “Africa Solar Belt” da kuma taimakawa Afirka ainun da ta hau tafarkin samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da rage fitar hayakin carbon.
Wang ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ganawarsa da shugaban Jamhuriyar Congo Denis Sassou Nguesso.
Da aka tambaye shi game da yadda kasar Sin da kasashen Afirka ke yin hadin gwiwa wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi, Wang ya ce, yadda shugaba Sassou ya mai da hankali sosai kan batun sauyin yanayi ya nuna hangen nesa na shugabannin Afirka, inda ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan Afirka a ko da yaushe wajen samun ci gaba ba tare ga gurbata muhalli ba, yayin da karfin tashar samar da wutar lantarki bisa hasken rana da bangarorin 2 suka yi hadin gwiwar ginawa ya zarce GW 1.5, wanda ke haskaka dubban gidaje a fadin nahiyar.
Wang ya kara da cewa, kasar Sin za ta aiwatar da shirin hadin gwiwa na samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka wajen gudanar da ayyukan makamashi mai tsafta da aka gabatar a taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing. (Mohammed Yahaya)