A gefen taron wakilan kungiyar ma’aikatan doka ta kasar Sin karo na 9, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kana shugaban kasar, Mr. Xi Jinping ya aika da wasika ga taron, inda ya mika gaisuwa ga masanan ilmin dokoki da ma masu ayyukan dake shafar dokoki na kasar, tare da gabatar da burin da yake so a cimma ta fannin dokoki.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, tun bayan taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kungiyoyin ma’aikatan doka na matakai daban daban sun hada kan masu aikin doka na kasar wajen gudanar da dimbin ayyuka, wadanda suka samar da gudummawa a fannin gudanar da harkokin kasar bisa doka.
A yau Jumma’a da safe ne aka bude taron wakilan kungiyar ma’aikatan doka ta kasar Sin karo na 9 a nan birnin Beijing, inda aka karanta wasikar da Xi Jinping ya aika. A gun taron, an kuma karrama fitattun sassa da mutane masu ayyukan doka na kasar. (Lubabatu Lei)