Kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wasikar da wasu matasa ’yan wasa a gidan wasan Peking Opera na kasar Sin suka aika masa. A daidai lokacin da ake cika shekaru 70 da kafuwar gidan, yana mai bayyana kyakkyawan fata, da gaisuwa ga ’yan wasan.
A cikin wasikar tasa, Xi Jinping ya bayyana fatansa ga masata ’yan wasan da su gaji nagartattun fasahohi, da al’adu daga magabata a wannan bangare, tare da yin kirkire-kirkire, ta yadda za su taka rawarsu ga fadada bunkasuwar al’adun kasar.
An ba da labarin cewa, kwanan baya, matasa ’yan wasa na gidan wasan Peking Opera na kasar Sin sun rubuta wata wasika ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, inda suka yi masa bayani kan yadda suke gado, da habaka wannan al’ada ta gargajiya, tare da bayyana niyyarsu ta yayata sha’anin wasan Peking Opera, da fadada nagartattun al’adun gargajiya na kasar Sin. (Amina Xu)