Rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin (PLA ) dake gabashi ta ci gaba da gudanar da atisaye da ba da horo na hadin gwiwa jiya a kewayen ruwa da sararin samaniyar tsibirin Taiwan kamar yadda aka tsara.
Wadannan atisayen sun fi mayar da hankali ne kan ayyukan hadin gwiwa na yaki da jiragen ruwa da hare-haren da ake kaiwa a kan teku.
Rundunar sojin ruwa ta tura da dama daga cikin jiragen ruwa, da jiragen yaki, da jiragen harba makamai masu linzami, a wani aikin hadin gwiwa na jiragen ruwan yaki dake karkashin teku.
Jiragen sintirin yaki dake karkashin teku, da jiragen ruwa na yaki, da jirage masu saukar ungulu, sun yi hadin gwiwa wajen atisayen.
Wadannan sun hada da binciken karkashin ruwa, da hare-haren takalar abokan gaba, da ayyukan tsaro. (Ibrahim Yaya)