An bukaci Gwamnan Jihar Filato, Barista Cale Manasseh Mutfwang, da ya yi takatsantsan da ‘yan barandan siyasa, ka da su hana shi gudanar da kyawawan manufofin da ya kudiri aniyar aiwatar wa al’ummar jihar.
Wannan kira ya fito ne daga bakin daya daga cikin dattawan garin Jos, Alhaji Iliyasu Muhammad, a lokacin da take zantawa da wakilimmu a makon da ya gabata. Ya ce sai ya yi hattara da ‘yan barandan siyasa a jihar wajen samun nasarar aiwatar da alkawuran da ya yi wa al’ummar jihar a lokacin yankin neman zavensa.
Ya yaba wa gwamnan bisa nasarorin da ya samu na maido da zaman lafiya tsakanin noma da makiyaya da rikici ya ki ci ya ki cinyewa a jihar na tsawon lokaci, amma sai ga shi a cikin dan karamin lokaci da ya yi da fara jan ragamar jihar an sami nasarar kwantar da rikicin.
Ya nemi al’ummar jihar da su manta da duk wani bambanci da ke sakaninsu su hada kansu su mara wa gwamnan baya don ya sami damar gudanar da ayyukansa cikin nasara.