Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakolo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma na yau da kullum. Tsokacimmu na yau zai yi duba ne game da rashin tsaftar cikin gida wadanne irin cututtuka ke haifarwa?
Usman Sani
Rashin tsaftar cikin gida yana haifar da kananan cututtuka ta hanyar jawo yaduwar kwayoyin cuta, kamar su kwayoyin da ke haddasa ciwon ciki, zazzavi, da gudawa. Guraren da ba a tsaftace ba suna jan hankalin kwari da dabbobi masu dauke da kwayoyin cuta.
-  Ali Nuhu Ya Zama Jakadan Kamfanin Tsaftace HaÆ™ora A Arewacin NijeriyaÂ
- Gudummawar Sin Ga Aikin Samar Da Duniya Mai Tsafta Da Kyan Gani
Wadanne hanyoyi za a bi don magance su?
Za a iya magance cututtukan da rashin tsafta ke haifarwa ta hanyar tsaftace muhalli akai-akai, amfani da ruwan sha mai tsabta, da tsaftace hannaye kafin cin abinci da bayan amfani da bayan gida. Haka nan, sanya shara a wuraren da suka dace da kuma tsaftace jikin dabbobin gida na taimakawa.
Sajida Ahmad Ibrahim
Assalamu alaikum. Cututtukan da rashin tsaftar cikin gida take haifarwa.
Maleriya, kwalara, Tayipot, Amai, Godawa, cutar ciwon san yi da dai sauransu.
Ya kamata mu dage da tsaftace mahallimmu domin rashin tsafta gaskiya ba karamar illa bace kai zama a iya kiran rashin tsafta ba karamar masifa bace, ban da cututtuka da yake haifarwa, rashin tsafta ta kan sa mutane su rika kyamarka, rashin tsafta har aure yake kashewa.
Hanyoyin magance wannan cututtuka:
- wanke hannu bayan an fito daga bayan gida, wanke hannu kafin a ci abinci, sannan a yi Bisimillah. Â
- Tsabtace ruwa kafin a yi amfani da shi a sha ko a yi girki.Â
- Wanke bandaki akai-aka domin gujewa cututtuka.Â
- Rufe abinci da tsabtace shi.Â
- Kwana da gidan sauro ko wajen da ke da sauro.Â
- Gyara kwatoci domin gujewa taruwar sauro
- Shara da wanke wanke domin gujewa taruwa kananan cuta da ba’a ganinsu.
- Rufe abinci da abin sha domin kada kudaje masu yada cutar kwalara su shiga ciki.
Hajiya Rukayya
Assalamu Alaikum Warahmatullah.                 Â
Gaskiya rashin tsaftar cikin gida na haifar da kanana da manyan cututtuka, Dalili kuwa shi ne, za ka ga mace ta fita gida tsaf amma cikin gidanta da kazanta, ga wanke-wanke ta barshi kuda na ta bi ga wanki ta jika yana ta wari, ga tsakar gidanta duk shara wanda hakan yana haifar da cututtuka irinsu Kwalara da Maleriya da dai sauransu don Allah mata mu gyara.
Daga Bilkisu Isma’il
Assalamu alaikum!
A gaskiya rashin tsafta cikin gida ba karamar cuta bace, saboda yana haifar da cututtuka da dama. Misali kamar Maleriya, Tayipot, Kwalara wato amai da gudawa cutar ciwon san yi na mata wanda wannan gaskiya ba karamar cuta bace, saboda idan cutar ta yi yawa har yana kai ga ya tava mahaifar mace, ki ga an zo ana ta wahala, wata ki ga ya zo ya kai ga har ana cewa ba za ta iya samun ciki ba saboda cutar ciwon san yi ya ci karfinta ya kashe mata mahaifa.
Wani sai ki ga an je asibiti ana cewa sai an yi mata wankin mahaifa, sai ki ga wata idan Allah ya sa an dace shikenan ta samu lafiya, wata kuma a yi ta yi har a gaji a barta. To kin ga gaskiya duka wadannan cututtuka da na lissafo ba kananu bane.
Ya kamata mata mu rage san jiki mutashi mu gyara gidajan kullum kar mu bar gidajanmu da kazanta. Ita kazanta tana kawo tsana tsakaninki da maigida koda kuwa shi bashi da tsafta, duk namiji ba ya san kazamar mace sai yaji duk tafita a ransa, mata mu gyara.
Hanyoyin da za ki gyara ki zama mai tsafta: Za ki iya kasa aikin gidanki, tsari ne abin, duk abin da kika yi amfani da shi kar ki bari wai sai kin zo shara a’a ki gyara wajen da take sai ki ga gidanki ba zai vaci ba. Kuma kullum ki kasance kina yi shara, ki koya wa ‘ya’yanki.
Sannan kar ki zama mai tara wanke-wanke, saboda shima babbar kazanta ce wani abu zai iya zuwa ya yi ta lasa miki kwano baki sani ba.
Faddausi Dahiru
Assalamu alaikum!
Rashin tsafta cikin gida gaskiya yana haifar da cututtuka da dama kuma banya cututtuka wadanda za su iya kashe mutum ma idan ba a yi taka tsantsan ba, kamar su Kwalara: Kwalara tana iya kashe mutum idan ya zo da karar kwana ki ga mutum yana ta amai da gudawa, mutum ya kare ya lalace cikin kwana guda idan Allah ma ya sa zai samu lafiya kenan, amma ana wahala idan ta kama mutum.
Maleriya: itama idan ta kama mutum, har ma idan ta ci karfin mutum ta wuce 1+, ana wahala za ki ga bata jin magani har sai an hada da allura.
Sai Tayipot shima idan ya kama mutum yana wahalar da shi. Abin da ke kawo shi rashin tsaftar ruwa, ko ka sha ruwa marar kyau ko kuma abin da a ka zuba ruwan bashi da kyau dayan biyu ne. Suna da yawa cututtukan, mata ya kamata mu daure, mu dage mu kuma jajirce wajen tsaftace muhallimmu, ke kanki idan kin tsaftar gidanki za ki ga kina yi jin dadin zama a ciki, sannan kuma iskar ma da za ta shigo za ki ji ta ta dabance mai dadi, babu wani wari.