Tsohon firaministan kasar Masar Essam Sharaf ya bayyana wa wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a kwanakin baya cewa, shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya ta kawo moriya ga bunkasuwar kasar Masar.
Sharaf ya yi nuni da cewa, a matsayinsa na farfesa na jami’a, abokansa daga sauran jami’o’i da dama sun gaya masa cewa, sun kafa hulda tare da bangaren kasar Sin, da kafa dakunan gwaji na hadin gwiwa a wasu fannoni. A ganin Sharaf, wannan halin musamman ne na kasar Sin, wato ba ma kawai samar da gudummawa ba, har ma da more fasahohinta da sa kaimi ga raya su da samun nasara a kansu. Kasar Sin tana kokarin taimakawa sauran kasashe wajen inganta fasahohi da yin kirkire-kirkire, babu shakka za a samu nasarori a nan gaba. An kafa babban dandalin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa a sakamakon raya shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya, wadda ya shafi fannonin jigilar kaya, da shimfida hanyoyin motoci, da jigilar kaya cikin jiragen ruwa, da gina hanyoyin jiragen kasa da sauransu, kana an raya shawarar don sa kaimi ga yin hadin gwiwa da juna, ba ma a fannin tattalin arziki kadai ba, har ma a fannin al’adu da sauransu. Kasar Sin ta riga ta kasance kasa abar misali wannan fanni, domin yayin da kasar Sin take kiyaye samun bunkasuwa kanta, tana son yin mu’amala da hadin gwiwa da sauran kasashen duniya baki daya. (Zainab Zhang)