“Ana sa ran zurfafa bunkasar dangantakar abokantaka mai moriyar juna tsakanin Sin da Afirka”, “Kasar Sin ta yi alkawarin ba da goyon baya ga kasashen Afirka wajen karfafa matakan tsaro”, “Kasar Sin na adawa da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen Afirka”…wadannan kalamai ne da kafofin yada labaran Afirka da dama suka bayyana kan ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai nahiyar Afirka, wadda ya kammala a yau 11 ga wata.
Wadanda ke bibiyar harkokin diflomasiyya na Sin sun san cewa, ministan harkokin waje ya kan kai ziyararsa ta farko nahiyar Afirka a kowace shekara, al’adar da ta shafe shekaru 35 tana ci gaba da gudana. Bana ce ta cika shekaru 25 da kafuwar taron dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) kuma shekara ta farko da aka fara aiwatar da sakamakon taron kolin na Beijing. Don haka ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai kasashen Namibia, da Jamhuriyar Kongo, da Chadi da Najeriya a farkon wannan shekara, ba wai kawai ta maimaita abun da kasashen Sin da Afirka suka saba yi a baya, wato ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan kai ziyararsa ta farko nahiyar Afirka a kowace shekara ba, har ma ta sa kaimi ga aiwatar da sakamakon da aka cimma na taron kolin Beijing.
A yayin wannan ziyararsa a Afirka, ministan harkokin wajen kasar Sin ya mai da hankali kan hadin gwiwa a fannonin tsaro da samun ci gaba da kasashen Afirka. Alal misali, kasar Sin ta ba da shawarar cewa, za ta ba da goyon baya ga kasashen Afirka wajen warware matsalolin Afirka ta hanyar Afirka, da kuma daukar kwararan matakai don taimakawa kasashen Afirka wajen daidaita batutuwan da suka haifar da rashin tsaro. Kasar Sin a shirye take ta daidaita karfinta da kasashen da abin ya shafa wajen kokarin samun damar yin hadin gwiwa a sabbin fannoni kamar makamashi mai tsafta, da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba a fannin ma’adanai da hada-hadar kudi, da taimakawa kasashen Afirka wajen bin hanyar samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba da rage fitar iskar carbon. Akwai kalaman da ke cewa, bunkasuwar hadin gwiwar Sin da Afirka ba wani yunkuri ne na tilasta wa Afirka bukatunta ba. A maimakon haka, ta mayar da hankali kan mayar da martani ga buri da damuwar ci gaban Afirka bisa ka’idar samun moriyar juna da samun nasara tare. (Mohammed Yahaya)