A shekarar bana, a karon farko kafar CMG za ta watsa bikin murnar sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, innda za ta shirya, da kuma yi amfani da fasahar zamani, don hidimtawa mutane masu bukata ta musamman, wato makafi da kurame, ta yadda za su nishadantu yayin wannan gagarumin biki.
An dai saba gabatar da wannan biki ne a jajiberin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wanda ke kunshe da wake-wake, da raye-raye, da sauran shirye-shirye masu kayatarwa. Har ila yau, an gabatar da bukukuwan har sau 42, kuma a shekarar 2014, an shigar da shi cikin manyan ayyukan kasar Sin.
A gwajin shiryawa karo na 2 da aka yi, ’yan wasa sun yi magana ta nuni da hannu, a cikin shirye-shiryen da aka gabatar, ciki har da raye-raye da wake-wake. Ban da wannan kuma, bisa gayyatar da aka yi musu, mutane masu bukata sun kai ziyarar inda ake shiryawa shirye-shirye, don a ji ra’ayoyinsu da nufin kara kyautata bikin. A bana, mutane masu bukata ta musamman fiye da miliyan 45, za su more wannan kasaitaccen biki. (Amina Xu)