Ofisoshin kula da harkokin Taiwan da na yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, sun wallafa wata takardar bayani mai taken “Batun Taiwan da dunkulewar kasar Sin a sabon zamani” a yau Laraba.
An fitar da takardar ne domin jaddada Taiwan a matsayin wani bangare na kasar Sin, da kuma bayyana matsayin JKS da al’ummar Sinawa game da kudurinsu na dunkule kasar, tare da nanata matsayi da manufofin JKS da gwamnatin kasar a sabon zamani.
A cewar takardar, tun asali, Taiwan yankin ne mallakar kasar Sin. kuma wannan batu ne dake da ingantaccen tubali na tarihi da doka.
Haka kuma, kudurin babban zauren MDD mai lamba 2758, wani daftari ne da ya tanadi manufar kasar Sin daya tilo, wanda karfin dokar dake tattare da shi, bai bayar da wata kafa ta shakku ba, kazalika, an yi ammana da shi a fadin duniya.
Bugu da kari, takardar ta ce, manufar kasar Sin daya tak, na wakiltar daukacin matsayar kasa da kasa, kuma ta yi daidai da ka’idar huldar kasa da kasa. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)