Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar, Xi Jinping ya zanta da babban sakataren jam’iyyar kwaminis ta kasar Vietnam, To Lam, ta wayar tarho a yau Laraba.
A zantawar tasu, shugaba Xi ya yi kiran samar da wani hadin kai a tsakanin Sin da Vietnam da za a gina dandalin bullo da sabbin ingantattun ayyukan hadin gwiwa tare da kafa wani tsari na masana’antu da samar da kayayyaki a tsakaninsu.
Kazalika, duk dai a yau din, shugaba Xi Jinping ya kuma tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka, Anura Kumara Dissanayake, wanda yake ziyarar aiki a birnin Beijing na kasar Sin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)