Hukumar wanzar da zaman lafiya ta Jihar Kaduna ( Kaduna State Peace Commission ) Ta bayyana cewa, matsalar rikice-rikicen Ƙabilanci da na Fulani Makiyaya da Manoma yanzu ya zama tarihi a faɗin jihar baki ɗaya.
Muƙaddashiyar Mataimakiyar Shugabar Hukumar, Hajiya Khadija Hawaja Gambo ce ta tabbatar da hakan yayin taron bita akan ayyukan hukumar na shekaru biyar da suka gabata tare da wasu kungiyoyin wanzar da zaman lafiya a jihar Kaduna, wanda ya gudana a ɗakin taro na gidan Hassan Usman Katsina da ke Kaduna.
- Sin A Shirye Take Ta Shawo Kan Sabani Tare Da Sabuwar Gwamnatin Amurka
- Jami’o’in Sin Da Najeriya Sun Yi Kira Da A Yaukaka Fahimta Tsakanin Al’adun Kasashe Masu Tasowa
Hajiya Gambo, ta ce “Yau fiye da Shekaru Biyar ba a samu matsalar ɓarkewar rikice-rikicen kabilanci ko Fulani makiyaya da manoma ba, wanda hakan ya furu ne bisa jajircewar hukumarmu wajen samun haɗin kan ɗaukacin al’ummar jihar Kaduna.
“Nasan yanzu an manta shekarar da aka samu rikicin kabilanci ko Fulani makiyaya da manoma a kaduna kuma idan babu hadin kan mutane, ba za mu samu wannan nasarar ba, wannan yana nuna cewa kowa yana da rawar takawa, ba wai kawai nauyi ne da ya rataya akan hukumarmu ba har da ma hada hannu da shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki wajen samar da tsare-tsaren wanzar da zaman lafiya. Muna aiki ba dare ba rana don neman zaman lafiya ya dore acikin al’ummar jiharmu”.
“Don haka, a yanzu Kaduna duk wani rikicin kabilanci ya zama tarihi, muna fata, jihar Kaduna ta zama abin koyi ga sauran jihohin da ke fama da irin wannan matsalar, su samu ilimin yadda muka yi muka warware namu matsalar, saboda haka, mu kullum a shirye muke wajen tabbatar da cewa an samu hadin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummarmu baki daya”.
A nata jawabin, babbar Daraktar kungiyar wayar da kan mata ta jihar Kaduna, Misis Hannatu Aruwan, ta bayyana gamsuwarta dangane da matakan da hukumar wanzar da zaman lafiya ta jihar Kadauna ke aiwatarwa wajen kara hada kan daukacin alummar jihar.
Akan hakan, Hannatu Aruwan ta bukaci gwamnatin jihar Kaduna da ta kara tallafa wa hukumar da kudade wajen ci gaba da kokarinta na wanzar da zaman lafiya da hadin kan al’umma wajen warware duk wata matsala da ke barazana ga wanzar da zaman lafiya a jihar.