Jami’an Hukumar Hana Da Sha Da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa sun kama wani nau’in Loud, wani nau’in tabar wiwi da aka boye a cikin kwano, wanda aka shirya don fitar da shi kasar Ingila a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.
Wata sanarwa da kakakin hukumar Femi Babafemi ya fitar ta ce an boye fakiti shida na sinadarin da ke dauke da nauyin kilogiram 3.50 a cikin kwano.
- Yawan Fasinjojin Da Jiragen Kasa Suka Dauka Ya Zarce Miliyan 200 A Lokacin Bikin Bazara A Kasar Sin
- Yawan Fasinjojin Da Jiragen Kasa Suka Dauka Ya Zarce Miliyan 200 A Lokacin Bikin Bazara A Kasar Sin
A cikin bayaninsa, Austin Balogun, wanda shi ne babban wakilin da ya dauki Sunday Adakole, ya yi ikirarin cewa an biya shi Naira 700,000 don jigilar kayan zuwa kasar Burtaniya, amma ya kashe wasni kaso daga cikin kudin wajen gudanar da ayyukan fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, kuma mafi yawa ya biya kudin Apartment,” Babafemi ya kara da cewa.
A wani samame kuma, Babafemi ya ce an kama wasu mutane biyu masu suna Joseph Adewale da Biodun Adelakun a Igbo Olumo da ke unguwar Ikorodu a Legas, a lokacin da jami’an NDLEA suka kai farmaki maboyarsu.
Babafemi ya bayyana cewa an gano lita bakwai na skuchies, wani sabon sinadari na psychoactibe da aka samar da black currant, wiwi da opioids.
“Sauran abubuwan baje kolin da aka kwato daga hannun mutanen biyu sun hada da: bindigogi guda uku da aka kera a cikin gida; bindiga guda da aka yi a gida guda biyu; bindigar zamani guda daya; bindigar gida guda daya; cartridges guda uku da 9mm mara komai da gatari mai kan karfe.
“Wani farmakin da aka kai Legas, ya kai ga kama skunk mai nauyin kilogiram 47, wani nau’in tabar wiwi, da kuma Nitrous Odide mai nauyin kilogiram 25.46 da aka fi sani da dariya a unguwar Akala da ke Mushin,” Babafemi ya kara da cewa.
A Jihar Ekiti, Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Adepoju Taiwo, dauke da kilo 1.950 na Canadian Loud a Iworoko Road, Ilokun, Ado-Ekiti, babban birnin jihar. ‘Yansanda sun kama Sani a ranar Litinin, 20 ga watan Janairu a Bode Saadu da ke Karamar Hukumar Moro a Jihar Kwara. An kwato kwayoyin Tramadol 50,000 na tramadol 225mg masu nauyin kilogiram 36.56 daga gare shi.
“Wata ‘yar Nijar mai suna Abubakar Lami mai shekaru 45 tare da wasu mutum biyu: Abba Sani mai shekaru 35 da Auwal Aliyu mai shekaru 32, jami’an NDLEA ne suka kama su a Gadar Tamburawa Kano, yayin da skunk mai nauyin kilogiram 13.1.
An samo wani sabon abu na psychoactibe daga wurinsu. Sanarwar ta kara da cewa, a garin Gefen Kasa da ke yankin Karamar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano, wata tawagar jami’an hukumar NDLEA sun gano wata gonar tabar wiwi tare da lalata wani mutum da ake zargi mai suna Sabo Ali Muhammad mai shekaru 45 da haihuwa da alaka da gonar.
Babafemi ya bayyana cewa an gano lita bakwai na skuchies, wani sabon sinadari na psychoactibe da aka samar da black currant, wiwi da opioids.