A jiya Asabar kasar Amurka ta sanar da kakaba karin harajin kwastam na kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka. Dangane da batun, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta bayyana rashin jin dadi da kin amincewa daga bangaren Sin.
Cikin sanarwar da ma’aikatar ta gabatar, ta ce matakin Amurka ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda ba zai ba da damar daidaita matsalar da kasar Amurka ke fuskanta ba, maimakon haka, zai lalata huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. Ban da haka, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta ce, kasar Sin za ta kai kara ga kungiyar cinikayya ta duniya, da daukar matakai don mayar da martani ga matakin Amurka.
A sa’i daya kuma, kasar Amurka ta ce za ta sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 25%, kan kayayyakin da take shigowa da su daga kasashen Mexico da Canada. Ban da haka, shugaban kasar Donald Trump ya ce yana duba yiwuwar kakaba karin haraji kan kayayyakin da ake shigar da su kasar Amurka daga kasashen Turai, ganin yadda kungiyar kasashen Turai EU ta hana shigowar motoci da amfanin gona na kasar Amurka cikin kasuwannin kasashen Turai, a lokacin da ya yi hira da ‘yan jaridu a kwanan baya. (Bello Wang)