Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen samun jinkirin saukar samun ruwan sama a jihohin da ke Arewaci da tsakiyar kasar a lokacin damina ta bana (2025).
An yi hasashen samun jinkirin saukar ruwan sama a jihohin da suka hada da Filato, wasu sassan Kaduna, Neja, Benuwe, Nasarawa, Taraba, Adamawa, da Kwara.
NiMet ta kuma yi hasashen saukar damina da wuri a jihohin Delta, Bayelsa, Ribas, Anambra, da kuma sassan Oyo, Ogun, Osun, Ondo, Legas, Edo, Enugu, Imo, da Ebonyi.