Babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Cai Qi, ya yi kira a ranar Laraba, da a ci gaba da yin kokari wajen kawar da ayyukan da ba su da ma’ana, da rage nauyin da ke wuyan jami’an kananan matakai, don tabbatar kyakkyawan salon aiki tsakanin ’yan jam’iyya da jami’ai wajen cimma burin da aka sa a gaba a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025.
Cai, wanda kuma mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ne, kuma mamba a sakatariyar kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a wani taro na matakin koli game da wannan batu.
Taron ya bayyana cewa, ya kamata a mayar da hankali wajen magance matsalolin da ke gaban jami’an matakin farko, hakazalika, ya kamata a kara himma wajen rage aikin cike takardu da tarurrukan da ba a bukata, da daidaita duk wani nau’i na bincike, dubawa da nazari, da daidaita ayyukan da suka shafi murnar bukukuwa, nune-nune da tarurruka. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp