Kasancewar Nijeriya daya daga cikin manyan kasashe a nahiyar Afirka da kuma yawan al’ummar da kasar take da shi ya sa ake samun ‘yan wasa da dama a kasar, sannan kuma har ila yau ake samun wasu ‘yan wasan da suke barin kasar ko kuma iyayensu su haife su a wasu kasashen amma kuma duk da haka wasu su dawo su wakilci kasarsu ta asali yayin da wasu kuma suka zauna su buga wasa a kasashen da iyayensu suka haife su.
‘Yan Nijeriya kuma masu goyon bayan tawagar kwallon kafa ta kasa Super Eagles sun dade suna nuna rashin jin dadinsu kan tawagar, kan yadda take gaza taka rawar gani a gasanni ko dai na nahiyar Afirka ko ma a matakin duniya, la’akari da yadda wasu kasashen da ba su kai Nijeriya ‘yan wasa ba amma idan ana buga wasannin kasashen suna ba wa mara da kunya.
- Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano
- Saudiyya Ta Yi Watsi Da Shirin Fitar Da Falasdinawa Daga Gaza
Tawagar Super Eagles ta ja zare a shekarun baya, inda ake yi wa tawagar kallon babba kuma mafi kwazo a nahiyar Afirka, musamman bayan lashe gasar Olympic da aka yi a Atalanta a shekarar 1996, inda kasar ta doke Brazil da Argentina a kan hanyarta na lashe gasar a kasar Amurka. Sai dai daga biya harkokin kwallon kafa da tawagar ke yi ya samu koma-baya, inda wasu tawagogin nahiyar suka fara nunawa Nijeriya yatsa.
Sai dai a lokuta da dama, akan dora laifin rashin nasarar tawagar kasar nan a kan ‘yan wasa, inda wasu ke ganin suna nuna kwarewa a kungiyoyinsu na Turai, amma da zarar sun koma gida, sai su zama tamkar ba su ba kuma wannan zargi yana nan a zukatan ‘yan Nijeriya wanda goge shi za iyi matukar wahala idan har ba wata gagarumar nasara Nijeriya ta samu ba ta ‘yan shekaru a kwallon kafa.
Nijeriya na cikin kasashen duniya da suke da zaratan ‘yan kwallo da suke nuna bajinta a kwallon kafa a Turai amma duk da haka akwai wasu zaratan ‘yan kwallo da asalinsu ‘yan Nijeriya ne, amma suke wakiltar wasu kasashen daban duk da cewa ba wani laifi bane amma da a ce wadannan ‘yan wasa suna wakiltar Nijeriya da an samu manyan nasarori a kwallon kafar kasar nan.
Ga wasu manyan ‘yan kwallo da tauraronsu ke haskawa a duniya, wadanda asalin ‘yan Nijeriya ne, wato ko dai iyayensu baki daya ko wani daga cikin iyayen ‘yan Nijeriya ne.
Jamal Musiala (Jamus)
Matashin dan wasa Jamal Musiala, wanda aka haifa a ranar 26 ga Fabrairun shekarar 2003, fitaccen dan kwallon kasar Jamus ne da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta Jamus din kuma yana cikin matasan ‘yan kwallon da suke tashe a duniya a yanzu saboda ba za ka lissafa matasan ‘yan wasa guda biyar ba a duniya ba tare da ka saka sunansa ba. An haife shi ne a garin Stuttgart da ke Jamus, amma mahaifinsa mai suna Daniel Richard asalin can Nijeriya ne, wanda ya yake da shaidar zama dan Ingila, mahaifiyarsa mai suna Carolina kuma ‘yar Jamus ce.
Matashi Musiala ya wakilci kasar Ingila a kwallon matakin yara, kafin ya koma Jamus da buga wasa sannan kuma ya lashe kofuna da dama irin su gasar Bundesliga guda hudu da sauran kofuna, sannan ya samu kyaututtuka da dama tun daga lokacin da kungiyar Bayer Munchen ta fara saka shi a wasa tun yana dan shekara 17 a duniya.
Karim Adeyemi
Karim-Dabid Adeyemi wanda aka haifa a ranar 18 ga watan Janairun shekarar 2002, dan wasan Jamus ne da kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund. An haifi dan wasan a birnin Munich, wanda mahaifinsa asalin dan Nijeriya ne, amma mahaifiyarsa ‘yar Romaniya ne kuma a kwanakin baya danwasan da ke buga wasa a Dortmund da ke Jamus ya kusa komawa kungiyar kwallon kafa ta Napoli ta kasar Italiya kafin daga baya cinikin ya rushe bayan yaki amincewa da tafiya.
A baya-bayan nan Karim Adeyemi ya bude wata gidauniya a Nijeriya kuma ya bude gidauniyar ne a birnin Ibadan da ke Jiyar Oyo a kudu maso yammacin kasar nan, inda ya ce gidauniyar za ta mayar da hankali kan koyar da wasanni da ilimi, sannan a lokacin da ya ziyarci Nijeriya, Adeyemi ya shaida wa manema labarai cewa nan gaba yana tunanin komawa buga wasa a gasar Premier ta Ingila.
Michael Olise
Shima matashin dan wasan an haife shi ne a ranar 12 ga Disamban 2001, dan kwallo da a yanzu yake wakiltar Faransa kuma yake buga wasa a kungiyar Bayern Munich ta kasar Jamus. Olise wanda ya koma Jamus da buga wasa daga kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace asalin mahaifinsa dan Nijeriya ne, amma mahaifiyarsa ‘yar Aljeriya ce mazauniyar Faransa. Kuma yanzu haka yana daya daga cikin matasan ‘yan wasan da tauraruwarsu take haskawa a nahiyar Turai.
Noni Madueke
Shi dai asalin sunansa shi ne Chukwunonso Tristan “Noni” Madueke, kuma an haife shi ne a ranar 10 ga Maris a shekarar 2002 kuma yanzu yana wakiltar kasar Ingila ne, sannan yana buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta Ingila kuma shima asalin mahaifinsa dan Nijeriya, amma shi a Ingila aka haife shi, sannan itama mahaifiyarsa ‘yar asalin kasar Ingila ce.
Bukayo Saka
Bukayo Saka fitaccen dan kwallo ne da a yanzu yake jan zarensa a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal da ke Ingila kuma danwasan wanda asalin sunansa Bukayo Ayoyinka Temidayo Saka, iyayensa Adenike da Yomi Saka duka ‘yan Nijeriya ne kuma a baya ya sha bayyana cewa yana alfahari da kasancewarsa dan Nijeriya, kuma ya kan ziyarci kasar nan a wasu lokutan.
Ethan Chidiebere Nwaneri
Ethan Chidiebere Nwaneri wanda aka haifa a ranar 21 ga watan Maris na 2007, matashin danwasa ne da a yanzu yake tashe a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, kuma an haife shi ne a arewacin Landan, amma iyayensa ‘yan Nijeriya ne, sannan ya wakilci tawagar ‘yanwasan kasa da shekara 16 da 17 da 19 sai dai har yanzu ba wakilci babbar tawagar Ingila ba, wanda hakan ya sa za a iya gayyatarsa Nijeriya.
Joshua Orobosa Zirkzee
Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bologna dake kasar Italiya, Joshua Orobosa Zirkzee wanda aka haifa a ranar 22 ga Mayun 2001, dan kwallo ne da yake wakiltar kasar Netherlands, kuma yake buga wasa a yanzu a kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta Ingila sanann an haife shi ne a birnin Schiedam, sai dai shi mahaifiyarsa ce ‘yar Nijeriya, amma mahaifinsa dan Netherland ne.